KDAI: Kungiyar Dattawan Arewa sun yi wa Buhari mubaya’a

KDAI: Kungiyar Dattawan Arewa sun yi wa Buhari mubaya’a

- Wasu Dattawan Arewa sun bayyana Buhari a matsayin zabin su

- Kungiyar KDAI ta zare hannu daga goyon bayan da aka ba Atiku

- Paul Tarfa yace Buhari ya fi dacewa da ya cigaba da mulki a 2019

KDAI: Kungiyar Dattawan Arewa sun yi wa Buhari mubaya’a

Dattawan Arewa sun barranta daga Kungiyar NEF a zaben 2019
Source: Twitter

Yayin da babban zaben 2019 ya gabato, mun samu labari cewa wasu Dattawan Najeriya a karkashin lemar Kungiyar Dattawan Arewa Initiative watau KDAI sun nuna cewa su na tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Dattawan na Arewa na KDAI, Kungiyar Dattawan Arewa Initiative sun bayyana cewa ba su tare da tafiyar Farfesa Ango Abdullahi na kungiyar NEF watau Northern Elders Forum wanda ya nuna goyon baya ga Alhaji Atiku Abubakar.

KU KARANTA: PDP ta karbe ‘dinbin Magoya bayan Jam’iyyar APC daf da zabe

Kamar yadda mu ka samu labari daga jaridar The Nation, shugaban kungiyar ta KDAI watau Janar Paul Tarfa mai ritaya yace shugaba Muhammadu Buhari za su zaba ba ‘dan takarar babban jam’iyyar adawa ta PDP mai adawa ba.

Paul Tarfa ya bayyana wannan ne a lokacin da ya gana da manema labarai a babban birnin tarayya Abuja. Tarfa yace sun yi la’akari da irin halin da Najeriya ta ke ciki da kuma tarihin kasar da yanayin da kasar ta ke ciki a wannan lokaci.

A baya mun ji cewa kungiyar Dattawan Arewa da kuma wasu manyan Arewa na yankin Arewa ta tsakiya da wasu kungiyoyi na mutanen Kudu da su ka hada PANDEF da Ohanaze sun ce su na tare da Atiku.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel