Tsallake rijiya da baya: Mai neman kujerar Majalisa ya sha da kyar a Jihar Ondo

Tsallake rijiya da baya: Mai neman kujerar Majalisa ya sha da kyar a Jihar Ondo

Mun samu labari daga jaridar the Cable cewa ‘Dan takarar kujerar majalisar wakilai na tarayya a wani yanki na mazabar jihar Ondo ya tsallake rijiya da baya inda aka nemi a kashe shi a Ranar Juma’a.

Tsallake rijiya da baya: Mai neman kujerar Majalisa ya sha da kyar a Jihar Ondo

Tajudeen Adefisoye ya tsallake rijiya da baya da baya
Source: Facebook

Wasu ‘Yan bangar siyasa ne su kayi yunkurin ganin bayan Tajudeen Adefisoye, inda su ka kai wa tawagar sa hari a shekaran jiya inda su ka harbi mutane har 3 a tawagar sa. Yanzu haka dai da-dama sun samu rauni a harin.

Kamar tadda mu ka ji, wadannan ‘yan banga sun tare motocin ‘dan siyasar ne a lokacin da yake kan hanyar Adefisoye da ke cikin Ipogun a karamar hukumar Ifedore a Jihar Ondo/ Wadanda aka harba su na asibiti a halin yanzu.

KU KARANTA: Idanu na kan Tinubu domin ganin Buhari yayi nasara a Yankin Legas

Wani daga cikin wadanda aka harba ya cika kamar yadda mu ka ji. Sunan daya daga cikin Mabiyan ‘dan takarar da ya rasu shi ne Kayode Falusi. Kakakin yakin neman zaben ‘dan takarar, mai suna Oluyemi Fasipe, ya bayyana wannan.

Adefisoye yana neman kujerar majalisar tarayya ne na yankin Ifedore da Idanre a karkashin jam’iyyar SDP. Saura kiris dai da an ga bayan sa a wannan hari kwantar bauna da aka kai wa tawagar sa yayin wani yawon kamfe a yankin.

Yanzu dai an fadawa jami’an tsaro wannan labari inji Oluyemi Fasipe. Kwanan ne dai kuma ka ji cewa wani ‘dan sanda da ke cikin masu tsare Tajudeen Adefisoye ya harbi wani ‘dan acaba har lahira.

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel