Da duminsa: Jami'an tsaro sun yi awon gaba da kakakin yakin zaben jam'iyyar PDP

Da duminsa: Jami'an tsaro sun yi awon gaba da kakakin yakin zaben jam'iyyar PDP

Rahotannin da Legit.ng ke samu yanzu na nuni da cewa jami'an tsaro sun cafke mai magana da yawun kungiyar yakin zaben jam'iyyar PDP na jihar Kaduna a ranar Lahadi, 10 ga watan Fabreru. Wani jami'in jam'iyyar ya tabbatar da cewa, Ben Bako, daraktan watsa labarai da hulda da jama'a na kungiyar yakin zaben jam'iyyar PDP a jihar Kaduna.

An cafke Mr Ben da misalin karfe 11 na safiyar Lahadi a Kaduna.

Legit.ng Hausa ta ruwaito maku yadda aka hasko Mr Bako a cikin wan fai-fen bidiyo yana umurtar jama'a da su tayar da rikici idan har aka yi masu ba dai-dai ba a wajen za ben jihar Kaduna.

Sai dai har zuwa yanzu babu wani bayani kan gaskiyar dalilin cafke kakakin yakin zaben jam'iyyar ta PDP, ko kuma cafke shi na da alaka da wannan bidiyo.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Tankar man fetur ta kama da wuta, mutane 2 sun mutu, 6 sun jikkata

Yanzu yanzu: Hukumar tsaro ta SSS ta cafke kakakin yakin zaben PDP

Yanzu yanzu: Hukumar tsaro ta SSS ta cafke kakakin yakin zaben PDP
Source: Twitter

Rahotanni sun bayyana cewa wasu jami'an tsaro da ake kyautata zaton cewa jami'an tsaro na farin kaya SSS ne suka cafke Mr Bako tare da wucewa da shi Abuja.

Da ya ke tabbatar da wannan lamari, mataimakin daraktan watsa labarai da hulda da jama'a na yakin zaben PDP, Yakubu Lere, ya ce jami'an hukumar tsaro ta SSS ne suka yi awon gaba da Mr Bako zuwa Abuja.

Ya ce jam'iyyar za ta sanar da matsayarta kan wannan lamari a yammacin Lahadi.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel