Da duminsa: Gobara ta lakume kayan zabe a ofishin INEC na jihar Filato, duba hotuna

Da duminsa: Gobara ta lakume kayan zabe a ofishin INEC na jihar Filato, duba hotuna

- Gobara ta tashi a ofishin hukumar INEC, na karamar hukumar Qua'an Pan, jihar Filato, inda kayan zabe da dama suka kone kurmus

- Haka zalika gobarar ta kone katunan zabe na din-din-din (PVCs) da ba a kai ga karba ba da kuma wasu muhimman kayan zaben da har yanzu ba a gama bayyana su ba

- Wannan lamarin dai ya jawo koma baya ga shirye shiryen babban zaben da ake yi a karamar hukumar

Rahotannin da Legit.ng Hausa ta samu na nuni da cewa gobara ta tashi a ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, na karamar hukumar Qua'an Pan, jihar Filato, inda kayan zabe da dama suka kone kurmus.

Jami'in ilimantar da masu kad'a kuri'a da kuma hulda da jama'a na jihar, Osaretim Imaehorobo, ya tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ya aikewa gidan talabin na Channels a ranar Lahadi.

"Wani mai gadi ne da ya yi shaye-shaye ya jawo tashin gobarar," a cewar sanarwar.

A yayin da gobarar ta tashi a daren ranar Asabar, gaba daya ofishin ya kone kurmus tare da dukkanin wasu kayayyaki da ke ciki, da suka hada da kwalayen da ke dauke da takardun kad'a kuri'a da sauransu.

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Tankar man fetur ta kama da wuta, mutane 2 sun mutu, 6 sun jikkata

Da duminsa: Gobara ta lakume kayan zabe a ofishin INEC na jihar Filato, duba hotuna

Da duminsa: Gobara ta lakume kayan zabe a ofishin INEC na jihar Filato, duba hotuna
Source: UGC

Sauran kayayyakin da gobarar ta lakume sun hada da babban injin samar da lantarki mai cike da fetur, sabbin takardun rejistar masu kad'a kuri'a da dai sauransu.

Haka zalika gobarar ta kone katunan zabe na din-din-din (PVCs) da ba a kai ga karba ba da kuma wasu muhimman kayan zaben da har yanzu ba a gama bayyana su ba.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa hukumar gudanarwar ofishin bisa jagorancin babban sakataren mulki, Gbadamasi Rasheed, sun isa ofishin domin duba irin barnar da gobarar ta yi da kuma tattara rahoto kan hakan.

Wannan lamarin dai ya jawo koma baya ga shirye shiryen babban zaben da ake yi a karamar hukumar.

Duba hotunan gobarar:

Da duminsa: Gobara ta lakume kayan zabe a ofishin INEC na jihar Filato, duba hotuna

Da duminsa: Gobara ta lakume kayan zabe a ofishin INEC na jihar Filato, duba hotuna
Source: UGC

Da duminsa: Gobara ta lakume kayan zabe a ofishin INEC na jihar Filato, duba hotuna

Da duminsa: Gobara ta lakume kayan zabe a ofishin INEC na jihar Filato, duba hotuna
Source: UGC

Da duminsa: Gobara ta lakume kayan zabe a ofishin INEC na jihar Filato, duba hotuna

Da duminsa: Gobara ta lakume kayan zabe a ofishin INEC na jihar Filato, duba hotuna
Source: UGC

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel