Atiku ko Buhari: Zai yi wuya a iya hasashen waye zai yi nasara – Ekweremadu

Atiku ko Buhari: Zai yi wuya a iya hasashen waye zai yi nasara – Ekweremadu

Mataimakin shugaban majalisar dattijai, Sanata Ike Ekweremadu, ya ce abu ne mai matukar wuya a iya has ashen waye zai yi nasara a zaben shugaban kasa da za a yi tsakanin manyan ‘yan takara; shugaba Buhari na jam’iyyar APC mai mulki da Atiku Abubakar na jam’iyyar adawa ta PDP.

A cewar Ekweremadu, sanin wanda zai lashe zaben shugaban kasa tsakanin Atiku da Buhari zai yi wuya ne saboda yadda ‘yan takarar biyu ke da karfi da magoya baya.

Ekweremadu ya bayyana hakan ne yayin amsa tambayoyi daga ma su sauraron hirar da aka yi da shi a gidan Radiyon Urban FM 94.5 a jihar Enugu, a jiya, Asabar.

Da aka tambaye shi don yin has ashen wanda zai nasara tsakanin Atiku da Buhari a zaben da za ayi ranar 16 ga wata, Ekweremadu ya ce bisa la’akari da abubuwan da ke faruwa a siyasance, zai yi wuya a iya hasashen wanda zai yi nasara a tsakanin ‘yan takarar biyu.

Atiku ko Buhari: Zai yi wuya a iya hasashen waye zai yi nasara – Ekweremadu

Ekweremadu
Source: Depositphotos

A cewar sa, “bari na fada ma ku abinda yanzu haka ke faruwa. A shekarar 2015, jama’a bas u yiwa PDP uzuri ba, amma yanzu jam’iyyar ta farfado kuma za ta iya bayar da mamaki.

Idan aka yi la’akari da yakin neman zaben ‘yan takarar biyu, za a fahimci cewar kowannen sun a da jama’a.

DUBA WANNAN: Za mu rubanya adadin ma su cin moriyar N-power sau 3 - Osinbajo

“Takara ce mai zafi tsakanin Atiku da Buhari amma da yardar Allah jam’iyyar PDP ce za ta lashe zabe.

Ekweremadu ya kasance dan siyasa ma fi girma daga yankin kudu maso gabas na ‘yan kabilar Igbo da ke jam’iyyar PDP.

A kwanakin baya ne aka fara rade-radin cewar Ekweremadu ya fita daga jam’iyyar PDP tare da komawa jam’iyyar APC. Sai dai daga baya ya fito ya bayyana cewar yana nan daram a cikin jam’iyyar sa ta PDP.

Yayin hirar da aka yi da shi, Ekweremadu y ace ya zauna a PDP ne, duk da irin kalubalen da ya fuskanta domin ganin cewar ba a mayar da siyasar Najeriya mallakar jam’iyya guda ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel