Da duminsa: Tankar man fetur ta kama da wuta, mutane 2 sun mutu, 6 sun jikkata

Da duminsa: Tankar man fetur ta kama da wuta, mutane 2 sun mutu, 6 sun jikkata

- Mutane biyu sun mutu yayin da 6 suka jikkata a lokacin da wata babbarf tanka cike da man fetur ta fadi a kusa da sha-tale-talen Amawabia, jihar Anambra

- Kwamandan rundunar hukumar kiyaye hadura ta kasa FRSC reshen jihar, Mr Andrew Kumapayi, ya tabbatar da faruwar hatsarin

- Har zuwa yanzu da aka wallafa wannan lamarin, 'yan kwana kwana na ci gaba da kokarin kashe wutar da dakileta daga yaduwa

Mutane biyu sun mutu yayin da 6 suka jikkata a lokacin da wata babbarf tanka cike da man fetur ta fadi a kusa da sha-tale-talen Amawabia, kusa da masaukin gwamna a jihar Anambra, inda a nan take ta kama da wuta.

Wani da lamarin ya faru a gaban idanunsa, ya tabbatar da cewa tankar ta kama da wuta ne nan take.

Kwamandan rundunar hukumar kiyaye hadura ta kasa FRSC reshen jihar, Mr Andrew Kumapayi, ya tabbatar da faruwar hatsarin.

Ya bayyana cewa direban tankar da ta fadi ya bugi kuibin wata babbar mota da ke ajiye a kusa da wasu tanyu na sha-tale-talen Amawbia, a yayin da ya ke kokarin yin kwana da ita.

KARANTA WANNAN: Gaskiyar magana: Igbo za su yi da-na-sani idan har ba su zabi Buhari ba - APC

Da duminsa: Tankar man fetur ta kama da wuta, mutane 2 sun mutu, 6 sun jikkata

Da duminsa: Tankar man fetur ta kama da wuta, mutane 2 sun mutu, 6 sun jikkata
Source: UGC

Kumapayi ya ce 'yan mintuna kadan bayan faduwar motar, ta kama da wuta.

Ya yi nuni da cewa an garzaya da wadanda hatsarin ya rutsa da su zuwa asibitin koyarwa na jihar.

Ya kuma tabbatar da cewa akwai motoci da dama da suka kone tare da gidajen da ke kusa da inda tankar man ta kama da wuta.

Haka zalika, hatsarin ya shafi sashen tsaro na masaukin gwamnan.

Har zuwa yanzu da aka wallafa wannan lamarin, 'yan kwana kwana na ci gaba da kokarin kashe wutar da dakileta daga yaduwa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel