Gaskiyar magana: Igbo za su yi da-na-sani idan har ba su zabi Buhari ba - APC

Gaskiyar magana: Igbo za su yi da-na-sani idan har ba su zabi Buhari ba - APC

- Jam'iyyar APC ta ce idan har Igbo ba su zabi Buhari a ranar Asabar mai zuwa ba, to kuwa za su tafka babban kuskure da yin da-na-sani a rayuwarsu

- Haka zalika APC ta tabbatar da cewa tana da yakinin cewa Buhari ne zai samu nasara a zaben mai zuwa

- Ya ce zaben ne zai iya zama 'yar manuniya akan ko shiyyar Kudu-maso-Gabas za ta iya shugabantar kasar a 2023

Kodinetan matasan shiyyar Kudu-maso-Gabas na kungiyar yakin zaben dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar APC, Innocent Ojike ya ce idan har Igbo ba su zabi shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben ranar Asabar mai zuwa ba, to kuwa za su tafka babban kuskure da yin da-na-sani a rayuwarsu.

Ya bayyana hakan a ranar Asabar a wani taron manema labarai a Awka, babban birnin jihar Anambra.

Ya ce Igbo za su rasa wani tagomashi a siyasar kasar idan har ba su fito kwansu da kwarkwatarsu suka zabi jam'iyyar APC ba, yana mai tabbatar da cewa yana da kinin Buhari ne zai samu nasara a zaben mai zuwa.

KARANTA WANNAN: Zaben 16 ga Fabreru: Kai ke da nasara - Oba na Legas ya yiwa Buhari albishir

Gaskiyar magana: Igbo za su yi da-na-sani idan har ba su zabi Buhari ba - APC

Gaskiyar magana: Igbo za su yi da-na-sani idan har ba su zabi Buhari ba - APC
Source: UGC

Ya ce zaben ne zai iya zama 'yar manuniya akan ko shiyyar Kudu-maso-Gabas za ta iya shugabantar kasar a 2023.

Ya yi nuni da cewa Ndigbo sun yi "sun yi babban kuskure na kin zabar Buhari a 2015", yana mai cewa akwai bukatar al'ummar Igbo su jajurce don ganin cewa hakan ba ta sake faruwa ba a zaben ranar Asabar, 16 ga watan Fabreru da ke karatowa.

Ya kuma nuna takaicinsa akan yadda kuri'un shiyyyar Kudu-maso-Gabas ya zama mafi karanci a fadin kasar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel