Kamfen: Buhari ya bar Abuja zuwa Gusau

Kamfen: Buhari ya bar Abuja zuwa Gusau

A wata sanarwa da mai taimakawa shugaba Buhari a bangaren sadarwar zamani, Bashir Ahmad, ya fitar ba da jimawa, ya bayyana cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tashi daga Abuja zuwa Gusau, babban birnin jihar Zamfara, domin kaddamar da yakin zaben sa.

A jiya ne shugaba Buhari da tawagar yakin neman zaben jam'iyyar APC su ka ziyarci jihar Legas. Dubbban jama'a ne su ka fito domin tarbar shugaban kasar tare da mataimakinsa da kuma ragowar manyan 'ya'yan jam'iyyar APC da hadiman shugaban kasa da kuma 'yan kwamitin yakin neman zaben sa.

APC dai na fama rigingimun cikin gida a Jihar Zamfara da ke barazanar hana jam'iyyar tsayar da dan takarar gwmna.

Kamfen: Buhari ya bar Abuja zuwa Gusau

Kamfen din Buhari
Source: UGC

Ko a jiya, sai da aka jiyo gwamnan jihar Zamfara na barazanar cewar babu wanda ya isa ya gudanar da zabe a jihar matukar jam'iyyar APC ba ta dan takara.

DUBA WANNAN: Kamfen: Kanawa sun saka wa Ganduje sabon suna

Tuni dai wata kotun tarayya ta haramtawa hukumar zabe mai zaman kan ta karbar sunan dan takarar gwamnan jihar Zamfa a jam'iyyar APC. Hakan ya biyo bayan gazawar jam'iyyar wajen gudanar da sahihin zaben fidda dan takarar gwamna saboda sabanin dake tsakanin shugabancin uwar jam'iyyar APC da gwamnatin jihar Zamfara.

Abun jira a gani shine ko wanne dan takarar gwamna, daga cikin ma su ikirarin cewar su ne 'yan takara, shugaba Buhari zi daga hannun sa kuma ya bashi tuta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel