Ina nan a Jam’iyyar APC duk da an tsige takara ta – David Umaru

Ina nan a Jam’iyyar APC duk da an tsige takara ta – David Umaru

Sanatan da ke wakiltar yankin Neja ta gabas a majalisar dattawan Najeriya, David Umaru, ya bayyana cewa bai da niyyar barin jam’iyyar APC mai mulki duk da an hana sa takara a karkashin jam’iyyar.

Ina nan a Jam’iyyar APC duk da an tsige takara ta – David Umaru

David Umaru yace albarkacin Buhari zai sa ya zauna a APC
Source: Depositphotos

Kwanan nan ne wani Alkali na kotun tarayya da ke Abuja ya karbe tikitin da aka ba Sanatan da ke kan kujerar na mazabar Neja ta Gabas ya mikawa Alhaji Sani Musa, a matsayin ainihin wanda yayi nasara a zaben fitar da gwani na APC.

Duk da wannan cikas da Sanatan ya gamu da shi ana shirin zabe a kasar yace bai da niyyar sauya-sheka. Sanata Umaru ya fadawa ‘yan jarida wannan ne bayan Alkali Giwa Ogunbanjo na kotu ya dauko wannan mataki kwanaki.

KU KARANTA: Babu zabe a Zamfara idan aka hana APC takara inji Yari

Sanata David Umaru ya bayyana cewa alakar sa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ta sa ba zai bar jam’iyyar mai mulki ba ba. Sanatan na Neja yace tun 2007 watau shekaru fiye da 10 da su ka wuce kenan yake tare da Buhari a siyasa.

Umaru ya fadawa menama labarai cewa bayan irin kyakkyawar dangantakar sa da shugaba Muhammadu Buhari, ya kuma yi la’akari da abin da mutanen mazabar sa za su inda yake ganin ba su ji dadi idan ya bar APC ba.

‘Dan majalisar yake cewa duk da ba a ga maciji tsakanin sa da gwamnan jihar Neja mai-ci watau Abubakar Sani Bello, ba zai fice daga jam’iyyar APC mai mulki wanda a cewar sa da gumin irin sa aka kafa ta a shekarun baya ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel