2019: Babban Jigon APC Bola Tinubu ya sha alwashin casa Atiku

2019: Babban Jigon APC Bola Tinubu ya sha alwashin casa Atiku

Mun ji labari cewa babban kusa a jam’iyyar mai mulki a Najeriya, Asiwaju Bola Tinubu ya bayyana cewa za su koyawa Atiku Abubakar wanda shi ne ‘dan takarar jam’iyyar adawa ta PDP darasi a zaben bana.

2019: Babban Jigon APC Bola Tinubu ya sha alwashin casa Atiku

Kusa a Jam’iyyar APC Tinubu ya nemi a zabi Buhari a Legas
Source: UGC

Bola Tinubu ya dauki lokacin sa wayar da kan jama’a game da zaben da za ayi kwanan nan a lokacin da shugaban kasa Buhari ya kai ziyarar kamfe zuwa jihar Legas. Tinubu yayi kira ga jama’a su sake zaben shugaba Buhari a bana.

Kamar yadda mu ka ji, Bola Tinubu ya fadawa mutane cewa su yi ta-ka-tsan-tsan wajen kada kuri’a saboda sashen da ake diba na kowace jam’iyya bai da girma a dalilin adadin jam’iyyun siyasar da ake da su a kasar a zaben bana.

Asiwaju Tinubu ya ja hankalin jama’ a da cewa su tabbatar sun zabi jam’iyyar APC a mako mai zuwa. Tsohon gwamnan na Legas ya kuma fadawa mutane cewa su tanadi guzurin abincin su a ranar zabe domin kuwa abin na yi ne.

KU KARANTA: Legas ta APC ce haka APC ta Legas ce a 2019 – inji Tinubu

Sarkin yakin neman zaben na shugaba Buhari ya fadawa mutanen sa cewa su yi amfani da yatsar su wajen ganin sun tika Atiku Abubakar na jam’iyyar hamayya da kasa a zaben. Tinubu yace yana son ya koyawa Atiku darasi ne a siyasa.

Tinubu yake cewa jama’a su dage wajen ganin na’urar nan ta PVC ta tantance su, sannan sai su nemi jam’iyyar APC mai alamar tsintsiya su dangwala mata da manuniyar yatsar su domin ganin jam’iyyar PDP ta sake kai kasa a zaben bana.

Jigon jam’iyyar mai mulki ya kuma fadakar da mutane cewa babu wanda ya isa ya hana su kada kuri’ar su a ranar zabe, sannan kuma ya ce su guji amfani da tawada sosai domin gudu a kasa kirga kuri’ar su.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel