Daruruwan Mabiyan APC sun kama tafiyar Jam’iyyar PDP a Jihar Filato

Daruruwan Mabiyan APC sun kama tafiyar Jam’iyyar PDP a Jihar Filato

Kamar yadda mu ka samu labari ba da dadewa ba daga jaridun Najeriya, wasu dinbin magoya bayan jam’iyyar APC mai mulki a jihar Filato da ke tsakiyar Najeriya sun sauya-sheka zuwa PDP kwanan nan.

Daruruwan Mabiyan APC sun kama tafiyar Jam’iyyar PDP a Jihar Filato

Magoya bayan APC sun sauya-sheka zuwa PDP a Jos
Source: UGC

Wasu manyan APC da ake ji da su a karamar hukumar Jos ta kudu da ke cikin Filato sun fice daga jam’iyyar ne, su ka koma PDP. Wadanda su ka sauya shekar sun bayyana cewa babu abin da za su samu a cikin tafiyar APC.

Wadannan masu sauya-sheka sun bayyana cewa za su hada kai da ‘dan majalisar tarayya na jihar da ke yankin watau Honarabul Edward Pwajok SAN, wajen ganin jam’iyyar PDP ta kai labari a zaben 2019 da ya karaso a kasar.

KU KARANTA: Gwamnan Kaduna El-Rufai yace ba ya gudun ya sha kasa a zaben 2019

Shi ma dai Edward Pwajok, yana cikin wadanda su ka tsere daga APC su ka koma jam’iyyar PDP kwanakin baya. ‘Yan siyasar sun bayyana cewa da su za ayi kokarin ganin PDP ta ci zabe daga sama har kasa a jihar ta Filato.

Kamar yadda mu ka ji labari, wadannan ‘yan siyasa sun fice daga jam’iyyar ta APC ne a jiya inda su ka koma PDP mai adawa a jihar Filato da nufin ganin jam’iyyar ta karbe mulkin jihar da kuma Najeriya baki daya a zaben bana.

Wani tsohon ministan wasannin kasar watau Damishin Sango ne ya karbi wadanda su ka sauya-shekar. Sababbin shiga PDP din sun fara yi wa Jeremiah Useni da kuma Atiku Abubakar kamfe tuni domin kasar ta dawo kan hanya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel