Ana sa rai APC za tayi kokari a zaben bana fiye da yadda tayi a 2015 a Kudu ta Yamma

Ana sa rai APC za tayi kokari a zaben bana fiye da yadda tayi a 2015 a Kudu ta Yamma

Ku na sana cewa a jiya ne jirgin yakin neman zaben shugaban kasa Buhari ya shiga jihar Legas inda shugaban kasar yake neman tazarce, har kuma ya kaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin jihar tayi.

Ana sa rai APC za tayi kokari a zaben bana fiye da yadda tayi a 2015

Jirgin yakin neman zaben shugaban kasa Buhari a Legas
Source: UGC

Masana harkar siyasa a Najeriya sun bayyana cewa akwai babban aiki a gaban shugaban kasar da jam’iyyar sa ta APC mai mulki wannan karo ma dai a jihar Legas da daukacin yankin na kudu maso yammacin kasar nan a zaben na bana.

Buhari ya saba zuwa na biyu ko na uku a yankin na kasar yarbawa a zaben da yake takara. Wannan karo APC ta karbi mulki inda kuma kasar Yarbawa ne ke da mataimakin shugaban kasa da manyan ‘yan siyasa na APC irin su Bola Tinubu.

KU KARANTA: Jam'iyyar APC ba za tayi takara a wasu Jihohi a zaben 2019 ba

A zaben 2015, shugaba Buhari ya samu nasara ne a kusan kaf jihohin Yarbawa face Ekiti inda Goodluck Jonathan ya kawo. Sai dai duk da haka ba wani tazaran a zo a gani a ka samu tsakanin APC da PDP a wancen zaben da aka yi ba.

Wadanda su ka san harkar siyasa sun bayyana cewa wannan karo dole sai Bola Tinubu wanda jigo ne a jam’iyyar APC kuma asali ma shi ne Sarkin yakin neman zaben Buhari a Najeriya, yayi da gaske wajen ganin PDP ta sha kashi a Yankin.

Haka kuma sai mataimakin na shugaba Buhari watau Yemi Osinbajo ya kara kaimi na ganin APC ta samu nasara a kudu maso yammacin kasar. Jaridar Saturday Vanguard tace ya zama dole jam’iyyar APC tayi wa Buhari aikin a zo a gani a bana.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel