Ba na jin tsoron fadi zaben Gwamnan Kaduna inji Nasir El-Rufai

Ba na jin tsoron fadi zaben Gwamnan Kaduna inji Nasir El-Rufai

Mun samu labari a jiya cewa mai girma gwamnan jihar Kaduna watau Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya nuna cewa sam ba ya gudun ya sha kasa a zaben gwamnonin jihohi da za ayi a watan gobe a Najeriya.

2019: Ba na jin tsoron fadi zaben Gwamnan Kaduna inji El-Rufai

Ba na tsoron zaben 2019 don na kori malamai a Kaduna – El-Rufa’i
Source: Facebook

Gwamnan na jam’iyyar APC mai mulki wanda yake neman komawa kan karagar mulki ya bayyana cewa bai yi nadamar matakan da ya dauka a kan kujerar da yake kai ba. Gwamnan yace don haka ba ya shakkar ya sha kasa a zaben bana.

Gwamna Nasir El-Rufai yace yana aiki ne domin mafi yawan jama’a su amfana ba wai don wasu tsirarrun al’ummar jihar ba. El-Rufai ya bayyana wannan ne lokacin da ya zanta da gidan jaridar BBC Hausa a cikin karshen makon nan.

KU KARANTA: Masu aikin N-Power za su zabi Shugaba Buhari a zaben 2019

Nasir El-Rufai ya kara da cewa ba zai dauki kudin al’umma ya rika ba wasu manyan gari ba, domin jama’a ya sa a gaba. Gwamnan na Kaduna ya kuma kare matakin da ya dauka na sallamar malaman makaranta a jihar inda yace hakan ya dace.

Malam El-Rufai yace wadanda aka kora daga aiki jahilai ne wadanda sam bai dace su rika koyawa yara karatu ba. Gwamnan yake cewa da-dama na wadanda ake cuta a kan hakan su ne ‘ya ‘yan talakawa marasa galihu da ke jihar Kaduna.

Gwamnan jihar ta Kaduna Nasir El-Rufai dai ya kori malaman makaranta fiye da 20, 000 kwanaki inda ya maye gurbin su da wadanda ake tunani sun fi cancanta. Gwamnan yace duk da zabe ya karaso, ba ya nadamar matakin da ya dauka.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel