Karya-ta-kare: Rundunar sojin Najeriya ta soma sintiri na musamman kan hanyar Abuja

Karya-ta-kare: Rundunar sojin Najeriya ta soma sintiri na musamman kan hanyar Abuja

Rundunar sojojin saman Najeriya tare da taimakon sojojin kasa da sauran hukumomin tsaro sun fara kaddamar da wani samame na tsoratarwa a hanyar Kaduna zuwa Abuja gurin da ya yi kaurin suna wajen yin garkuwa da mutane da fashi da makami.

An kaddamar da samamen na dai yau a wani kauye da ake kira Katari dake zaman matattarar miyagun mutane, kauyen da ya yi kaurin suna wajen bada mafaka wa masu aikata miyagun laifuka, kuma a samamen na yau da aka kaddamar an yi nasaran kama wasu tsageru.

Karya-ta-kare: Rundunar sojin Najeriya ta soma sintiri na musamman kan hanyar Abuja

Karya-ta-kare: Rundunar sojin Najeriya ta soma sintiri na musamman kan hanyar Abuja
Source: Twitter

KU KARANTA: Wani dan PDP ya debo ruwan dafa kan sa a Kaduna

Legit.ng Hausa ta samu cewa kamar yadda rundinar sojin saman Nijeriya ta ce wannan samamen da ta shirya yana matsayin gargadi ne ga miyagun mutane masu aikata munanan laifuka akan hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Hanyar dai ana yawan aikata laifin yin garkuwa da mutane matafiya, da kuma fashi da makami, akwai tsageru a kayukan dake kan hanyar wadanda suke haddasa kashe-shen al'umma, kamar yadda kwamandan da ya jagoranci kaddamar da samamen wato Wing Commander Leonard Onugha ya bayyana.

Kamar dai yadda muka samu, rundinar zata cigaba da kaddamar da samamen har sai an kawar da burbushin masu aikata miyagun laifuka akan hanyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel