Ba a isa ayi zabe ba a Zamfara idan har aka cire APC – Gwamna Yari ga INEC

Ba a isa ayi zabe ba a Zamfara idan har aka cire APC – Gwamna Yari ga INEC

Gwamna Abdul’Aziz Yari Abubakar na jihar Zamfara ya yi barazaar cewa babu zaben da za a yi a jihar idan har hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta cire yan takarar jam’iyyar All Progressive Congress (APC) daga cikin zaben kasar mai zuwa.

Gwamna Yari ya bayyaa hakan a ranar Juma’a, 8 ga wata Fabrairu lokacin gangamin jam’iyyar APC a karamar hukumar Talata Mafara a ci gaba da gangamin zabensa a ke gudana a jihar.

“Babu yadda za a yi a gudanar da zabe a jihar Zamfara ba tare da yan takarar APC ba, duk da hukucin babbar kotun Zamfara da ta tabbatar da cewar APC ta gudanar da zaben fidda gwani a jihar”, Yari yayi gargadi.

Ba a isa ayi zabe ba a Zamfara idan har aka cire APC – Gwamna Yari ga INEC

Ba a isa ayi zabe ba a Zamfara idan har aka cire APC – Gwamna Yari ga INEC
Source: UGC

Yace haka zai zamo babban kuskure da barazana ga tsaro kasa idan gar INEC ta hana yan takarar APC a Zamffara takara a lokacin zabe mai zuwa a jihar.

KU KARANTA KUMA: Babu makawa Lagas ta APC ce – Tinubu

Yari ya bukaci masu zabe da su zabi Shugaban kasa Muhammadu Buhari da dukkanin yan takarar jam’iyyar APC a zabe mai zuwa.

INEC na na kan bakarta na cewa APC reshen Zamfara bata da yan takara saboda jam’iyyar bata gudaar da zaben fidda gwani ba saan bata gabatar da jerin sunaye ga hukumar ba a raar 7 ga watan Oktoba wanda shine ranar karshe da hukumar ta bayar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel