Yan Igbo za su yi danasani idan basu zabi Buhari ba - APC

Yan Igbo za su yi danasani idan basu zabi Buhari ba - APC

Shugaban kwamitin kamfen din dan takarar shugaba kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a kudu maso yamma, Innocent Ojike yace yan Igbo za su yi danasani idan har basu zabi shugaba kasa Muhammadu Buhari ba a zabe mai zuwa.

Ya bayyana hakan a ranar Asabar, 9 ga watan Fabrairu a wai taron manema labarai a Awka, babbar birnin jihar Anambra.

Yace yan Igbo za su rasa rabe-raben siyasar kasar ida har suka gaza zabar APC inda ya kara da cewa Buhari zai yi nasara.

Yan Igbo za su yi danasani idan basu zabi Buhari ba - APC

Yan Igbo za su yi danasani idan basu zabi Buhari ba - APC
Source: Twitter

Yace zabe ne zai bayyana matakin da kudu maso yamma za ta kasance a siyasar kasar a shekarar 2023.

Ya nuna bakin ciki cewa karfin zabe na yanki kudu maso yamma shine mai karanci a kasar.

KU KARANTA KUMA: Mun yi alkawari, kuma muna cikawa – Inji shugaba Buhari

Ya yi kira ga Buhari da ya samar da karin jiha idan yayi nasara a zaben mako mai zuwa.

A wani lamari na daban, mun ji cewa babban jigon jam’iyar All Progressives Cogress (APC) na kasa, Cif Bola Tinubu a ranar Asabar, 9 ga watan Fabrairu ya bukaci jama’a da su kada kuri’unsu ga APC a zabe mai zuwa. Yace babu makawa jihar Lagas tasu ce a zabe mai zuwa.

Yace gwamnatin Buhari tayi matukar kokari da dan kudade da albarkatun kasar cikin shekaru hudu kacal.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel