Babu makawa Lagas ta APC ce – Tinubu

Babu makawa Lagas ta APC ce – Tinubu

- Babban jigon jam’iyar APC na kasa, Cif Bola Tinubu ya bukaci jama’a da su kada kuri’unsu ga APC a zabe mai zuwa

- Tinubu yace babu makawa jihar Lagas ta jam'iyyar APC ce

- Yace gwamnatin Buhari tayi matukar kokari da dan kudade da albarkatun kasar cikin shekaru hudu kacal

Babban jigon jam’iyar APC na kasa, Cif Bola Tinubu a ranar Asabar, 9 ga watan Fabrairu ya bukaci jama’a da su kada kuri’unsu ga APC a zabe mai zuwa.

Da yake jawabi ga dandazon al’umma magoya bayan APC a filin wasa na Teslim Balogun, da ke Surulere, Lagas idan Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da kamfen dinsa na shugabanci kasa, Tinubu ya bayyana cewa jam’iyyar adawa a shekaru 16 da tayi kan mulki ta gaza kawo ci gaba duk da tarin albarkatun kasar.

Babu makawa Lagas ta APC ce – Tinubu

Babu makawa Lagas ta APC ce – Tinubu
Source: UGC

Yace gwamnatin Buhari tayi matukar kokari da dan kudade da albarkatun kasar cikin shekaru hudu kacal.

“Ranar yau ta kasance na damokradiya sannan kuma ba wai don Buhari kawai bane. Babu makawa Lagas ta jam’iyyar APC ce gaba daya a zabe mai zuwa.

KU KARANTA KUMA: Mun yi alkawari, kuma muna cikawa – Inji shugaba Buhari

“Dukkanin mutanen da ke a wannan tafiar sa sun raba wani bangare na wannan damokradiyar, ya zama dole mun inganta kayayyakin more rayuwa, wannan ne kadai mafita, sai mun samar da ayyuka,” inji Tinubu.

Yace Buhari a kamfen dinsa na 2015, yayi alkawari wanda ya kuma cika tun daga lokacin da hau kujerar mulki.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel