Mun yi alkawari, kuma muna cikawa – Inji shugaba Buhari

Mun yi alkawari, kuma muna cikawa – Inji shugaba Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Asabar, 9 ga watan Fabrairu ya kaddamar da hukumar karfafa ikon zuba jari na Najeriya (NSIA) da kuma cibiyar kula da cutar daji a asibitin koyarwa na jami’ar Lagas, domin tabbatar da cewar akwai isassun kayayyaki na magance cutar daji na matakin farko ga yan Najeriya.

A wajen taron, a Idi Araba, shugaba Buhari ya sanar da cewa za a kawo sunfuri a fadin kasar domin bayar da kulawa mafi inganci ga mutanen da ke fama da cutar daji a Najeriya.

Shugaban kasar ya bayyana cewa suna sane da makudan kudaden da yan Najeriya ke kashewa a kasashen waje domin magance cutar kansa.

Mun yi alkawari, kuma muna cikawa – Inji shugaba Buhari

Mun yi alkawari, kuma muna cikawa – Inji shugaba Buhari
Source: UGC

Yace duk da tarin mutane yan kasar da ke fama da wannan cuta na’urar kula da wannan cuta biyu ne kawai a kasar.

Yayinda yake yiwa ma’aikatan asibitin fatan alkhairi kan gudanar da cibiyar, shugaba Buhari ya jadadda cewa akwai bukatar a kula da kayayyakin aikin.

KU KARANTA KUMA: Zan aske gashin kaina idan Buhari ya ci zabe – Bello Muhammad Bello

Shugaban kasar yayi alkawarin cewa gwamnatinsa wacce ta gabatar da shirye-shirye na kawar da cututtuka, ciki harda samar da kudade don tabbatar da cewa dukkanin yan Najeriya na da damar ziyarta asibitocin gwamnati, za ta ci gaba da wayar da kan al’umma game da cutar kansa, da kuma taran cutar a matakin farko.

Ya bayyana cewa hakan na daga cikin alkawarin da suke kokarin cika wa yan Najeriya a shekaru hudu don inganta kulawar lafiya a kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel