Hatsarin mota: Hadiman gwamnan jihar Kogi 3 sun tsallake rijiya da baya

Hatsarin mota: Hadiman gwamnan jihar Kogi 3 sun tsallake rijiya da baya

Wasu hadiman gwamnan jihar Kogi guda uku sun tsira daga wani hadarin mota da su kayi a hanyar Obajana zuwa Kabba a hanyarsu ta zuwa Isanlu domin hallartar yakin neman zaben mata na APC.

Sanarwar ta fito ne daga bakin Mr Onogwu Muhammed sakataren yada labarai na gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi.

A cewarsa sanarwar, hadiman gwamnan sun hada da Mrs Kelechi Ajayi, mai bawa gwamna shawara a kan harkokin mata da yara; Mrs Ejura Edward, mai bawa gwamna shawara a kan harkokin mata, da Mrs Adesoro Olamide, hadimar matan gwamna na musamman a kan kafafen yada labarai.

DUBA WANNAN: Tsohon janar a rundunar soji ya kwance wa Obasanjo zani a kasuwa

Hadiman gwamnan jihar Kogi uku da su kayi hatsari sun tsira da ransu

Hadiman gwamnan jihar Kogi uku da su kayi hatsari sun tsira da ransu
Source: UGC

Gwamnatin na jihar Kogi ta mika godiyarta ga Allah saboda dukkan mutanen da ke cikin motar sun tsira da ransu kuma suna cikin koshin lafiya.

"Cike da godiya ga Allah, gwamnatin Jihar Kogi tana son amfani da wannan damar domin sanar da cewa dukkan hadiman gwamna da su kayi hatsarin mota sun tsira da rayukansu.

"Hadiman gwamnan a kan Mata da yara hada, Mrs Kelechi Ajayi da Hadiman matar Gwamna a an harkokin mata, Mrs Ejura Edward da mai taimakawa gwamna na musamman a kan kafafen yada labarai, Mrs Adesoro Olamide sun yi hatsarin mota a safiyar yau.

"Hatsarin motan ya faru ne kusa da kauyen Oshokoshoko a hanyarsu ta zuwa Isanlu domin hallartar taron mata amma duk sun tsira da ransu da lafiyarsu.

"Gwamnatin jihar tana mika godiyarta ga Allah da ya kiyaye wadanda hatsarin ya afka da su.

"Jirgin yakin neman zaben matar gwamna na gida zuwa gida za su cigaba da kamfen dinsu a mazabar Kogi ta Yamma bayan sunyi kwanaki biyu a mazabar Kogi ta Kudu," inji sanarwar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel