Hotuna: Yadda yakin zaben shugaban kasa Buhari ya ke gudana a Legas

Hotuna: Yadda yakin zaben shugaban kasa Buhari ya ke gudana a Legas

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da yakin zabensa a jihar Legas, domin fuskantar babban zaben 2019 da zai gudana a ranar 16 ga watan Fabreru. Shugaban kasar na neman takarar tazarce a karo na biyu, bayan darewa mulki a zaben 2015, ta hanyar tunkude mai mulki a lokacin, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dira jihar Legas da safiyar yau, a filin sauka da tashi na Murta Muhammad, inda daga bisani ya ziyarci fadar Sarkin Legas, Oba Rilwan Akiolu, ya kuma ziyarci gidan gwamnati sannan daga bisani ya gana da magoya bayansa a filin wasa na Teslim Balogun da ke Surulere domin isar da sakonsa na Next Level.

Daga cikin wadanda suka gabatar da jawabai akwai shi shugaban kasa Muhammadu Buhari, mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo; jagoran APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, da Chief Bisi Akande, da dai sauran manyan shuwagabannin jam'iyyar APC da masu ruwa da tsaki, a babban filin wasanni na Teslim Balogun.

Ga kadan daga cikin hotunan taron.

KARANTA WANNAN: Ranar Laraba: Abuja za ta cika makil saboda gangamin yakin zaben Atiku da Buhari

Hotuna: Yadda yakin zaben shugaban kasa Buhari ya ke gudana a Legas

Hotuna: Yadda yakin zaben shugaban kasa Buhari ya ke gudana a Legas
Source: Twitter

Jagororin jam'iyyar APC a lokacin yakin zaben Buhari a Legas

Dandazon jama'a sun halarci taron yakin zaben Buhari a Legas

Dandazon jama'a sun halarci taron yakin zaben Buhari a Legas
Source: Facebook

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel