Haraji: Gwamnatin Buhari za ta fara farautar attajiran Najeriya 85,000

Haraji: Gwamnatin Buhari za ta fara farautar attajiran Najeriya 85,000

Shugaban hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake da alhakin tattara harajin cikin gida watau Federal Inland Revenue Service (FIRS) a takaice, Tunde Fowler, ya bayyana cewa hukumar za ta fara farautar hamshakan attajiran da ke kin biyan harajin su.

Mista Tunde Fowler ya bayyana hakan ne lokacin da ya ke magana da Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Mohammed Adamu da ya kai masa ziyara a Abuja, inda ya ce sun gama shiri tsaf wajen haka hannu da ‘yan sanda, domin tilasta wa attajiran biyan haraji.

Haraji: Gwamnatin Buhari za ta fara farautar attajiran Najeriya 85,000

Haraji: Gwamnatin Buhari za ta fara farautar attajiran Najeriya 85,000
Source: Facebook

KU KARANTA: Shugaba Buhari yayi wa barayin Najeriya Allah-ya-isa

Legit.ng Hausa ta samu cewa Mista Tunde Fowler ya kara da cewa kwananan nan suka kammala tantance attajirai sama da 45,000, masu jarin sama da naira miliyan 100 a asusun ajiyar su na banki, inda aka tatsi harajin naira bilyan 23 a hannun su.

Ya ce akwai kuma wasu rukunin hamshakan allajiran har 40,000 da su ma ba su biyan haraji, wadanda za a hada hannu da ‘yan sanda, domin a tatsi haraji daga jarin kasuwancin su.

Fowler ya ce akwai kuma rukunin hamshakan attajirai wadanda jarin su ya kai naira milyan 999, wadanda su ma ana kan layin binciken asusun ajiyar su a bankuna daban-daban.

Wadanda ma ba su da lambar shaidar iznin harkokin kasuwanci ta TIN, inji Fowler, sun kai 45, 504, kuma ba su biyan kudaden haraji.

Gaba daya dai ya ce ya zuwa yanzu an samu attajirai 40,000 da ba su biyan haraji, wadanda ya ce cikin 2019 din nan za a fara farautar su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel