Buhari ya gana da hamshakan attajiran Najeriya a Legas, hoto

Buhari ya gana da hamshakan attajiran Najeriya a Legas, hoto

A yau Asabar 9 ga watan Fabrairu ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa a jihar Legas, inda ya kai ziyara jihar domin kaddamar da neman yakin zabensa, gabanin babban zaben ranar 16 ga watan Fabrairu.

A yayin ziyarar na shugaba Buhari, zai gana da jiga-jigan 'yan kasuwan Najeriya da suka hada da Alhaji Aliko Dangote shugaban rukunonin kamfanin Dangote da Mr Femi Otedola shugaban Forte Oil Plc da wasu kamfanonin.

Wasu na ganin wannan alama ce da ke nuna suna goyon bayan takarar na Shugaba Muhammadu Buhari a babban zaben da ke tafe.

Buhari ya gana da manyan 'yan kasuwan Najeriya a Legas

Buhari ya gana da manyan 'yan kasuwan Najeriya a Legas
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Buhari ya yi sabbin nade-nade 30 a RMAFC (jerin sunaye da mukamai)

Legit.ng ta samu wannan rahoton ne daga mai tallafawa shugaban kasar ta fuskar kafofin sadarwa na zamani Bashir Ahmad, wanda ya wallafa a shafinsa na twitter, a ranar Asabar, 9 ga watan Fabrairu, 2019.

Kafin saukar Buhari a jihar ta Legas, tuni aka tsaurara matakan tsaro a wuraren da shugaban kasar zai ziyara, musamman kuma babban filin wasanni na jihar, inda a nan ne zai kaddamar da yakin zaben na sa.

A na sa ran shugaban kasar zai kai ziyara fadar Sarkin Legas, Oba Rilwan Akiolu, ya kuma ziyarci gidan gwamnati sannan daga bisani zai gana da magoya bayansa a filin wasa na Teslim Balogun da ke Surulere domin isar da sakonsa na Next Level.

NAN ta ruwaito cewa dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar Progressives Congress (APC) a zaben ranar 16 ga watan Fabrairu, Muhammadu Buhari zai ziyarci Legas domin kaddamar da yakin neman zabensa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel