An kashe sojoji 3 a harin da Boko Haram ta kai sansanin soji a Borno

An kashe sojoji 3 a harin da Boko Haram ta kai sansanin soji a Borno

Sojoji uku ne suka rasu yayin da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai hari a wani sansanin sojoji da ke Arewa maso Gabashin Najeriya kamar yadda jami'an tsaro suka sanar a ranar Asabar.

An kai harin ne a sansanin sojoji na kauyen Ngwom da ke kilomita 14 Arewacin Maiduguri, babban birnin jihar Borno kamar yadda Punch ta ruwaito.

"Boko Haram sun kai farmaki a sansanin mu da ke Ngwom a jiya Juma'a misalin karfe shida da minti hamsin na yamma kuma sun rasa dakarun sojoji uku," a cewar wani soja da ya yi hira da AFP.

An kashe sojoji 3 a harin da Boko Haram ta kai sansanin soji a Borno

An kashe sojoji 3 a harin da Boko Haram ta kai sansanin soji a Borno
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Buhari ya yi sabbin nade-nade 30 a RMAFC (jerin sunaye da mukamai)

Wani majiyar daga sojin kuma ya ce 'yan ta'addan sun sace motoccin soji guda biyu sannan sun lalata mota mai bi ta kan nakiya guda daya.

"Sojojin sun kuma kone gidaje biyu da mota guda mallakar wani ma'aikacin mu," a cewar wani jagoran Civilian JTF da ke Maiduguri.

Ba a tabbatar ko wace bangare na kungiyar Boko Haram din ne suka kai harin ba.

Kungiyar ISWAP ce ta dauki nauyin kai mafi yawancin hare-haren da aka kaiwa sojojin da ke Borno da Yobe daga watan Yulin 2018.

Wasu hare-haren kuma mayakan kungiyar Boko Haram da ke biyaya ga Abubakar Shekau ne suka kai.

Duk da cewa rundunar sojin ba ta amince da cewa an kaiwa sojojin hari ba, akwai alamun har yanzu akwai sauran 'yan kungiyar da ke kai hari duk da cewa soji ta ce an ci galaba a kan 'yan ta'addan.

A kalla mutane 27,000 ne aka kashe a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya kuma wasu miliyan 1.8 sun rasa muhallinsu tun bullowar kungiyar ta'addan shekaru 10 da suka shude.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel