Buhari ba zai samu kaso 50 na kuri’u ba a Bauchi – Dan majalisa na APC

Buhari ba zai samu kaso 50 na kuri’u ba a Bauchi – Dan majalisa na APC

- Dan majalisar dokoki na jihar Bauchi, Aminu Tukur, ya sha alwashin cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari a zai samu kaso 50 na kuri’u ba a jihar Bauchi a zabe mai zuwa

- Tukur ya bayyana cewa Buhari ba zai samu irin goyon bayan da ya samu ba a baya daga jihar saboda goyon bayan Gwamna Mohammed Abubabakar da yayi

- Yace ko shi yana cikin wadanda ba za su sake zabar shugaban kasar ba

Wani dan majalisar dokoki na jihar Bauchi, Aminu Tukur, ya sha alwashin cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari a zai samu kaso 50 na kuri’u ba a jihar Bauchi a zaben Shugaban kasar da za a gudanar a ranar 16 ga watan Fabrairu.

Tukur ya bayyana cewa Buhari ba zai samu irin goyon bayan da ya samu ba a baya daga jihar saboda goyon bayan Gwamna Mohammed Abubabakar da yayi a matsayin dan takarar gwamnan jihar na APC a zabe mai zuwa.

Buhari ba zai samu kaso 50 na kuri’u ba a Bauchi – Dan majalisa na APC

Buhari ba zai samu kaso 50 na kuri’u ba a Bauchi – Dan majalisa na APC
Source: Twitter

Tukur wanda ke wakiltan mazabar Lere/Bula a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) yace, “Buhari ba zai iya yanke makomar mutanen jihar Bauchi ba, idan yana da kaso 90 na magoya baya a zaben 2015, toh wannan karon ko kaso 50 ba zai samu ba.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Kotu ta bayar da umurnin kama Ciyaman na CCB

“Tunda ya daga hannun Gwamna Moammed Abubakar, toh shi (Buhaari) ya kayar da kansa. Ko Shugaban kasar a zai sa ba a jihar Bauchi a wannan karon. Ina daya daga cikin wadanda ba za su zabe shi ba.”

Dan majalisar ya kuma zargi gwamnatin jihar da gaza isar sa damokradiya ga mutanen jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel