Ranar Laraba: Abuja za ta cika makil saboda gangamin yakin zaben Atiku da Buhari

Ranar Laraba: Abuja za ta cika makil saboda gangamin yakin zaben Atiku da Buhari

A ranar Laraba, babban birnin tarayya zai dauki amon tarurrukan siyasa, biyo bayan hukuncin da jam'iyyar PDP ta dauka na gudanar da babban gangamin yakin zaben dan takarar shugaban kasarta a ranar Laraba, bayan da aka hana ta gudanar da gangamin taron a tsohon filin atisaye na Garki, Abuja a ranar Asabar.

Laraba ce ranar da ita ma jam'iyyar APC ta tsaida domin gudanar da babban gangamin yakin zaben dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar.

A baya Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa jam'iyyar PDP ta dakatar da gangamin yakin zaben da ta shirya gudanarwa a babban birnin tarayya Abuja a ranar Asabar bayan da hukumar bunkasa birnin tarayya FCDA ta hana su tsohon filin atisaye na Garki, Abuja.

KARANTA WANNAN: Da zafinsa: PDP ta soke yakin zabenta na FCT Abuja da ta shirya gudanarwa yau Asabar

Ranar Laraba: Abuja za ta cika makil saboda gangamin yakin zaben Atiku da Buhari

Ranar Laraba: Abuja za ta cika makil saboda gangamin yakin zaben Atiku da Buhari
Source: Facebook

Daraktar sashen mulki da kudi, sakatariyar bunkasa ababen more rayuwa, hukumar da ke kula da tsohon filin atisayen na OPG, Hajiya Safiya Umar, ta tabbatar da cewa PDP ta amince ta matsar da gangamin yakin zabenta zuwa ranar Laraba, a wannan fili.

A wannan ranar, magoya bayan jam'iyyar APC za su taru domin yin gangamin yakin zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari a babban filin wasanni na kasa da ke Abuja. Filin wasannin na da karfin daukar mutane 60,000.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel