Da zafinsa: PDP ta soke yakin zabenta na FCT Abuja da ta shirya gudanarwa yau Asabar

Da zafinsa: PDP ta soke yakin zabenta na FCT Abuja da ta shirya gudanarwa yau Asabar

- PDP ta dakatar da babban yakin zabenta na shugaban kasa da ta shirya gudanarwa a yau Asabar, 9 ga watan Fabreru a birnin tarayya Abuja

- PDP ta ce wannan matakin ya biyo bayan hana jam'iyyar filin da zata gudanar da zaben

- Sai dai jam'iyyar ta yi fatan cewa yakin zaben da ta shirya gudanarwa a ranar Talata, 12 ga watan Fabreru a jihar Legas zai gudana ba tare da samun wata tangarda ba

Jam'iyyar PDP ta dakatar da babban yakin zabenta na shugaban kasa da ta shirya gudanarwa a yau Asabar, 9 ga watan Fabreru a birnin tarayya Abuja.

A cikin wata sanarwa daga daraktan watsa labarai na kungiyar yakin zaben dan takarar shugaban kasa karkashin jam'iyyar, Mr Kola Ologbondiyan a ranar Asabar a Abuja, PDP ta ce wannan matakin ya biyo bayan hana jam'iyyar filin da zata gudanar da zaben.

"Wannan ya faru duk da cewa PDP tuni ta biya kudade ga hukumomi tare da karbar dukkanin wasu takardu da ya dace na gudanar da wannan taron a tsohon filin atisaye na Garki, Abuja."

KARANTA WANNAN: Da duminsa: Dandazon jama'a sun marabci Buhari a lokacin da ya dira jihar Legas

Da zafinsa: PDP ta soke yakin zabenta na FCT Abuja da ta shirya gudanarwa yau Asabar

Da zafinsa: PDP ta soke yakin zabenta na FCT Abuja da ta shirya gudanarwa yau Asabar
Source: UGC

Ologbondiyan ya kara da cewa PDP a baya ta yanke shawarar gudanar da babban yakin zaben a filin wasanni na Tafawa Balewa da ke Legas a jihar Legas, kafin daga bisani APC ta ce itama a nan zata yi kuma a wannan rana, wanda ya tilasta PDP hakura.

Sai dai ya yi fatan cewa yakin zaben PDP da ta shirya gudanarwa a ranar Talata, 12 ga watan Fabreru a jihar Legas zai gudana ba tare da samun wata tangarda ba.

Ologbondiyan ya jinjinawa yunkuri da hakurin 'yan Nigheria musamman ma wadanda tuni suka sauka a birnin tarayya Abuja domin halartar babban gangamin yakin zaben jam'iyyar.

"A yayin da nauke baiwa kowa hakuri bisa faruwar wannan rashin mutuncin da fadar shugaban kasa da APC ta yi mana, za mu sauya ranar da zamu gudanar da gangamin nan ba da jimawa ba."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel