Da duminsa: Dandazon jama'a sun marabci Buhari a lokacin da ya dira jihar Legas

Da duminsa: Dandazon jama'a sun marabci Buhari a lokacin da ya dira jihar Legas

Labarin da Legit.ng ke samu yanzu na nuni da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dira filin sauka da tashi na jiragen sama a jihar Legas, inda ya kai ziyara jihar a domin kaddamar da neman yakin zabensa, domin fuskantar zaben ranar 16 ga watan Fabreru.

Legit.ng ta samu wannan rahoton ne daga mai tallafawa shugaban kasar ta fuskar kafofin sadarwa na zamani Bashir Ahmad, wanda ya wallafa a shafinsa na twitter, a ranar Asabar, 9 ga watan Fabreru, 2019.

Kafin saukar Buhari a jihar ta Legas, tuni aka tsaurara matakan tsaro a wuraren da shugaban kasar zai ziyara, musamman kuma babban filin wasanni na jihar, inda a nan ne zai kaddamar da yakin zaben na sa.

KARANTA WANNAN: Bayan tafiyar Buhari: Yan ta'adda sun farwa tawagar gwamnan jihar Taraba, Ishaku

Da duminsa: Dandazon jama'a sun marabci Buhari a lokacin da ya dira jihar Legas

Da duminsa: Dandazon jama'a sun marabci Buhari a lokacin da ya dira jihar Legas
Source: Facebook

A na sa ran shugaban kasar zai kai ziyara fadar Sarkin Legas, Oba Rilwan Akiolu, ya kuma ziyarci gidan gwamnati sannan daga bisani zai gana da magoya bayansa a filin wasa na Teslim Balogun da ke Surulere domin isar da sakonsa na Next Level.

NAN ta ruwaito cewa dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar Progressives Congress (APC) a zaben ranar 16 ga watan Fabrairu, Muhammadu Buhari zai ziyarci Legas domin kaddamar da yakin neman zabensa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel