CIkin Hotuna: Ganawar Atiku da manyan kungiyoyi 3 a jihar Benuwe

CIkin Hotuna: Ganawar Atiku da manyan kungiyoyi 3 a jihar Benuwe

A jiya Juma'a 8 ga watan Fabrairu, 2019, dan takarar kujerar shugaban kasa karkashin inuwa ta jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya gudanar da taron sa na yakin neman zabe cikin birnin Makurdi na jihar Benuwe da ke yankin Arewa ta Tsakiya a Najeriya.

Cikin jawaban sa ga a dumbin al'ummar da suka fito kwansu da kwarkwata domin nuna goyon bayan su a gare sa, Atiku ya sha alwashin tabbatar da tsaro da jin dadin rayuwar su tare inganta harkokin noma a yayin kasancewar sa shugaban kasa.

Yayin neman goyon baya, baya ga ziyarar ban girma da ya kai fadar Masarautar Benuwe, Atiku ya kuma halarci wani taron ganawa da al'ummar Hausawa da ke jihar. Ya kuma gudanar da wani taro na daban da kungiyar Kiristocin Najeriya reshen jihar.

KARANTA KUMA: Kamfe: Tururuwar al'umma yayin yakin zaben Atiku a jihar Katsina

Bayan tsakurowa daga zauren sada zumunta, jaridar Legit.ng ta kawo muku wasu kayatattun hotuna da ke nuna yadda Atiku ya gudanar da yakin sa na neman zabe wajen neman goyon bayan manyan kungiyoyin uku a jihar Benuwe.

Ganawar Atiku da al'ummar Hausawa ta jihar Benuwe

Ganawar Atiku da al'ummar Hausawa ta jihar Benuwe
Source: Twitter

Ganawar Atiku da al'ummar Hausawa ta jihar Benuwe

Ganawar Atiku da al'ummar Hausawa ta jihar Benuwe
Source: Twitter

Atiku yayin gabatar da jawaban sa ga al'ummar Hausawa ta jihar Benuwe

Atiku yayin gabatar da jawaban sa ga al'ummar Hausawa ta jihar Benuwe
Source: Twitter

Atiku a fadar Masarautar Benuwe

Atiku a fadar Masarautar Benuwe
Source: Twitter

Manyan Sarakuna a fadar masarautar Benuwe

Manyan Sarakuna a fadar masarautar Benuwe
Source: Twitter

Atiku yayin gabatar da jawaban sa ga kungiyar Kiristoci ta CAN reshen jihar Benuwe

Atiku a fadar masarautar Benuwe

Atiku a fadar masarautar Benuwe
Source: Twitter

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel