Kamfen din Buhari a Legas: An tsaurara matakan tsaro a filin tashi da saukan jirage

Kamfen din Buhari a Legas: An tsaurara matakan tsaro a filin tashi da saukan jirage

Rahoton da muka samu ya nuna cewa an baza jami'an tsaro masu yawa a wasu muhimman wurare a filin tashi da saukan jirage na Murtala Muhammed da ke Legas gabanin ziyarar da shugaba Muhammadu Buhari zai kai jihar domin kaddamar da yakin neman zabensa.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito cewa jami'an tsaron suna wuraren da aka ajiye su tun misalin karfe shida da rabi na safiyar yau.

Jami'an tsaron sun hada da 'Yan sanda, Sojojin Saman Najeriya, Jami'an Kwastam, Jami'an Immigration da kuma jami'an Hukumar tsaro ta NSCDC.

Kamfen din Buhari a Legas: An tsaurara matakan tsaro a filin tashi da saukan jirage

Kamfen din Buhari a Legas: An tsaurara matakan tsaro a filin tashi da saukan jirage
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Tsohon janar a rundunar soji ya kwance wa Obasanjo zani a kasuwa

Kazalika, akwai jami'an hukumar kiyaye hadurra na kasa FRSC da ke kulawa da shige da ficen ababen hawa a filin tashi da saukan jiragen da harabarsa.

NAN ta ruwaito cewa dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar Progressives Congress (APC) a zaben ranar 16 ga watan Fabrairu, Muhammadu Buhari zai ziyarci Legas domin kaddamar da yakin neman zabensa.

Shugaban kasar zai kai ziyara fadar Sarkin Legas, Oba Rilwan Akiolu, ya kuma ziyarci gidan gwamnati sannan daga bisani zai gana da magoya bayansa a filin wasa na Teslim Balogun da ke Surulere domin isar da sakonsa na Next Level.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel