Magu: Akwai matsala, yadda kudade ke yawo lokutan zabe, na magudi ne

Magu: Akwai matsala, yadda kudade ke yawo lokutan zabe, na magudi ne

- Magu ya koka akan hauhawar siye da siyarwar kuri'u a kasar nan

- Yace hakan kan kawo tawaya wajen zaben wadanda ya dace

- Ya hori manajojin masana'antun kudi dasu hada kai wajen ceto kasar nan daga wadanda ake zargin yan ta'adda ne

Magu: Akwai matsala, yadda kudade ke yawo lokutan zabe, na magudi ne

Magu: Akwai matsala, yadda kudade ke yawo lokutan zabe, na magudi ne
Source: Facebook

Ibrahim Magu, mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa ya koka akan cigaban siye da siyarwar kuri'a a zabe mai zuwa.

Magu ya sanar da hakan ne a ranar juma'a yayin taron shi da manajojin masana'antun kudi na Najeriya.

Anyi mishi take da: "wajibcin manajojin masana'antun kudi a Najeriya wajen kawo karshen siye da siyarwar kuri'u a zabe a Najeriya."

Magu yace shige da ficen kudi ba bisa ka'ida ba zai rage wadatuwa ga gwamnati wajen samar da ababen more rayuwa ga yan kasa. Siye da siyar da kuri'u wajen zabe zai iya hana yan takarar da suka dace shiga ofisoshin da suka kamata."

GA WANNAN: An kaddamar da jirgin kasan nan da kasar Yarabawa suka dade suna jira, nan gaba zai je har Daura

A Najeriya, siye da siyarwar kuri'u kullum hauhawa yake ta yadda ake siya ma'aikatan zabe, jami'an tsaro, masu lura da zabe kai har ma da kafafen yada labarai. Inji shi.

Magu yace a sakamakon hauhawar siye da siyarwar kuri'un ne har yanzu yan siyasa duke ciniki tare da kokarin kaiwa madogara a siye da siyarwar.

Ya hori manajojin masana'antun kudi dasu hada kai wajen ceto kasar nan daga wadanda ake zargin 'yan ta'adda ne.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel