Gwamnatin Tarayya ta rufe makarantun Unity Schools don zabukan makon gobe

Gwamnatin Tarayya ta rufe makarantun Unity Schools don zabukan makon gobe

- Ministan ilimi ya bayyana sanar da hutun tsakiyar zangon karatu na kananan makarantu zai zamo lokacin zabe ne

- Anyi hakan ne don saukakewa iyaye zuwa kada kuri'un su

- Ministan ya jinjinawa kungiyar malaman jami'o'i akan kishin kasa da suka nuna da gwagwarmaya don habakar ilimi

Gwamnatin Tarayya ta rufe makarantun Unity Schools don zabukan makon gobe

Gwamnatin Tarayya ta rufe makarantun Unity Schools don zabukan makon gobe
Source: Depositphotos

Ministan ilimi, Adamu Adamu, yace kananan makarantun fadin kasar nan zasu yi hutun tsakiyar zangon karatu tsakanin 15 zuwa 19 ga watan Fabrairu.

Kamar yanda ministan ya fada, hakan umarni ne don tabbatar da iyaye sun samu damar fita don kada kuri'un su a zaben shugabancin kasa da za'ayi a ranar 16 ga watan Fabrairu.

"Daliban mu na kananan makarantu basu kai shekarun da zasu yi zabe ba amma mun gyara hutun su na tsakiyar zangon karatu don ya fada lokacin zabe," hakan yace a takaitaccen bayanin da yayi wa manema labarai a ranar juma'a a Abuja.

"Ranakun hutun tsakiyar zangon karatun shine daga juma'a 15 zuwa talata 19 ga watan Fabrairu. Wannan hutun kananan makarantu ne a fadin kasar nan. Bazamu rufe sauran makarantu ba. Amfanin wannan hutun shine don iyaye su samu wadataccen lokaci don zuwa kada kuri'ar su kuma su samu damar maida yaran su makaranta,"

GA WANNAN: Wannan lamari yana daga min hankali matuqa-gaya - Abdulaziz Yari na Zamfara

"Koda yaran bazasu saka kuri'a ba, iyayen zasu saka. Hutun saboda zaben shugaban kasa ne. Babu hutun zaben gwamnoni."

Da yayi magana akan dakatar da yajin aikin malaman jami'a, ministan yace hakan gwagwarmaya ce don "cigaban tsarin ilimin kasar nan".

"Duk da fushi na da kosawa da ASUU, na jinjinawa kishin kasar su da suka bayyana saboda makonnin da suka gabata sunyi su ne wajen gwagwarmaya akan ilimi ba wai don kudi ba."

Ministan ya bayyana yakinin shi na cewa kungiyar malaman polytechnic ma zasu bi sahun na jami'ar nan ba da dadewa ba.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel