Shugabancin Atiku ne kadai zai iya kawo adin kai a tsakanin ‘yan Najeriya – Saraki

Shugabancin Atiku ne kadai zai iya kawo adin kai a tsakanin ‘yan Najeriya – Saraki

- Shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki ya jadadda cewa; shugabancin Atiku Abubakar ne zai kawo hadin kan ‘yan Najeriya

- Saraki yace dan takarar shugaban kasar na PDP zai samar da ayyukan yi tare da inganta tsaro idan har ya yi nasarar lashe zaben 2019

Shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki ya jadadda cewa; shugabancin dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party, Alhaji Atiku Abubakar ne zai kawo hadin kan ‘yan Najeriya.

Ya kara da cewa tsohon mataimakin Shugaban kasar zai kuma samar da ayyukan yi tare da inganta tsaro idan har ya yi nasarar lashe zaben 2019.

Shugabancin Atiku ne kadai zai iya kawo adin kai a tsakanin ‘yan Najeriya – Saraki

Shugabancin Atiku ne kadai zai iya kawo adin kai a tsakanin ‘yan Najeriya – Saraki
Source: Twitter

Saraki ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a, 8 ga watan Fabrairu a garin Makurdi, babbar birnin jiar Benue lokacin gangamin kamfen din Atiku da Obi wanda ya gudana filin wasa na Aper Aku.

Ya nemi masu zabe da su ba su goyon baya ta hanyar zaben dan takararsu, idan ya bukaci da su samu akalla kuri’u miliyan 2 cikin kuri’u miliyan 2.5 na jihar.

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Kotu ta bayar da umurnin kama Ciyaman na CCB

A nashi jawabin, shuhgaban PDP, Uche Secondus, ya ce; Atiku yana da kwarin guiwar kawo karshen rashin tsaro da ake fama da shi a kasarnan. Inda ya tabbatar da ‘yan Nijeriya cewa; idan har suka zabi Atiku, al’umma za su tsaro tare da walwala a kasar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel