Dalilai da za su sanya al'umma su sake zaben Buhari a 2019 - Mohammed

Dalilai da za su sanya al'umma su sake zaben Buhari a 2019 - Mohammed

- Ministan sadarwa da al'adu, Lai Mohammed ya ce salon mulkin shugaba Muhammadu Buhari ita za ta saka a sake zabensa

- Ministan ya yi wannan furucin ne a wata taro da tsaffin ma'aikata da masu karbar fansho na tsohuwar kamfanin Nigeria Airways suka shirya

- Mohammed ya kara da cewa shugaba Muhammadu Buhari ya kawo karshen jira na tsawon shekaru 14 da wahalhalu da tsaffin ma'aikatan kamfanin jirgin saman suka shiga

Ministan sadarwa da al'adu, Alhaji Lai Mohammed ya bayar da tabbacin cewa mayar da hankali a kan inganta rayuwa da jin dadin 'yan Najeriya da shugaba Muhammadu Buhari ya yi kawai da isa dalili 'yan Najeriya su sake zabensa a ranar 16 ga watan Fabrairu.

Ministan ya yi wannan furucin ne a wata taro da tsaffin ma'aikata da masu karbar fansho na tsohuwar kamfanin Nigeria Airways suka shirya a yau Juma'a a jihar Legas.

Dalilin da zai sa a sake zaben Buhari - Lai Muhammed

Dalilin da zai sa a sake zaben Buhari - Lai Muhammed
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Jigo a APC ya ce kowa ya zabi abinda ya ke so bayan zaben Buhari

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ta ruwaito cewa kungiyar ta shirya taron ne domin nuna godiyarta ga shugaban kasa Muhammadu Buhari sakamakon biyansu fanso da sauran alawus dinsu da suka kwashe shekaru 14 suna jira.

Sama da ma'aikata 5,000 na Nigeria Airways da suka ce gwamnatin baya ta wulakanta su tare da cin zarafinsu ne suka gudanar da tattakin na nuna goyon bayan Shugaba Muhammadu Buhari.

A jawabinsa, ministan ya ce shugaba Muhammadu Buhari ya kawo karshen wahalhalun da ma'aikatan tsohuwar kamfanin 5,996 suka kwashe shekaru 14 suna sha.

"Kowa ya san cewa tun bayan rushe Nigeria Airways, gwamnatocin da suka biyo baya sun gaza biya tsaffin ma'aikatan hakokinsu wanda hakan ya haifar musu da bakar wahala.

"Ba tsaffin ma'aikatan Nigeria Airways ne kadai suka amfana da shirye-shiryen inganta rayuwar al'umma na wannan gwamnatin ba.

"Tsaffin 'yan sanda na Biafra, tsaffin ma'aikatan kamfanin Delta Steel, Aladja da tsohuwar kamfanin NITEL suma duk sun sami hakokinsu da aka kwashe shekaru ba a biya su ba.

"Iyalan sama da ma'aikata 800 na Nigeria Airways da suka rasu za su karba hakokin da mahaifansu suka bari," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel