Da dumi-dumi: Kotu ta bayar da umurnin kama Ciyaman na CCB

Da dumi-dumi: Kotu ta bayar da umurnin kama Ciyaman na CCB

- Kotu ta bada umarnin kama ciyaman din CCB

- Kotun ta bada umarnin kamashi ne bayan yaki halartar gayyatar da tayi masa sau da dama

- Kotun ta bada umarnin a gabatar mata dashi a gabanta kafin 13 ga watan Fabrairu

A ranar Juma'a ne babbar kotun jihar Kaduna ta bada umarnin kama ciyaman din CCB saboda rainuwa.

Mai sharia Mario Mohammed ne ya bada wannan umarni bayan ciyaman din yaki halarta gayyatar da kotun tayi masa lokuta da dama.

Kamfanin Today publishing da gwamnan jihar Kaduna Mal.Nasir El- rufai da kuma wani guda daya sun shiga takun saka ne.

Da dumi-dumi: Kotu ta bayar da umurnin kama Ciyaman na CCB

Da dumi-dumi: Kotu ta bayar da umurnin kama Ciyaman na CCB
Source: Twitter

Takardar umarnin ta bawa jami'an tsaro damar kama ciyaman din sannan su gurfanar dashi a gaban kotun a ranar 13 ga watan Fabrairu da muke ciki.

KU KARANTA KUMA: Zaben 2019: Atiku, PDP na shirin shigo da makamai da kudade ta Kamaru - Nabena

Kamfanin Today Publishing wanda ke buga labarai ya nemi kotu ta sa ciyaman din kungiya CCB daya bayyana a gabanta domin ya gabatar da kadarorin da yayi furuci na gwamnan jihar Kaduna ne.

Rahoto ya bayyana cewa gwamnan jihar ta Kaduna Mal.Nasir Elrufai ya shigar da kara ne bisa wani rahoto da jaridar ta fitar na cewa yana da N90b a cikin kadarorin sa CCB.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel