Shugabanni a Kano sun roki baki yayinda tsoro ya cika zukatan mutane kan yiwuwar barkewar rikicin zabe

Shugabanni a Kano sun roki baki yayinda tsoro ya cika zukatan mutane kan yiwuwar barkewar rikicin zabe

Shugabanni a Kano sun ba wadanda ba asalin yan jihar bane tabbacin samun kariya da zaman lafiya, inda suka kara da cewa babu wani rikicin kabilanci da zai afku a jihar lokacin zaben kasar mai zuwa.

Shuwagabannin a karkashin kungiyar kabilu na jihar Kano wato Ethnic Community Leaders Association, Kano state (ECLAK), a ranar Juma’a, 8 ga watan Fabrairu sun bayar da tabbacin ne bayan wani ganawa da shugabannin gargajiya a jihar, jaridar Punch ta ruwaito.

Legit.ng ta tattaro cewa Shugaban ECLAK, Ayelangbe ne ya jagoranci taron sannan an gudanar dashi ne a fadar sarkin Igbo da ke Sabon Gari karamar hukumar Fagge da ke jiar Kano.

Shugabanni a Kano sun roki baki yayinda tsoro ya cika zukatan mutane kan yiwuwar barkewar rikicin zabe

Shugabanni a Kano sun roki baki yayinda tsoro ya cika zukatan mutane kan yiwuwar barkewar rikicin zabe
Source: Twitter

Kungiyar ta nuna kwarin gwiwar cewa akwai zaman lafiya mai inganci a tsakanin kabilu, sannan ta fada ma wadanda ba yan asalin jihar bane da kada su gudu su bar Kano, inda suka basu tabbacin samun ingantaccen tsaro domin a tanadi duk wani matakai na tsaro da zai kare su da dukiyoyinsu.

KU KARANTA KUMA: Zaben 2019: Atiku, PDP na shirin shigo da makamai da kudade ta Kamaru - Nabena

A wani lamari na daban, mun ji cewa kasar Amurka ta bayyana cewa sakamakon zaben gama gari da za'a gudanar nan ba da dadewa a tarayyar Najeriya yana da matukar muhimmaci a gareta da ma dukkan daukacin kashen duniya baki daya.

Jakadan kasar ta Amurka a kasar Najeriya Mista Stuart Symington shi ne ya bayyana hakan jim kadan bayan ya kammala wata ganawar sirri da gwamnan jihar Nasarawa, Gwamna Tanko Al-makura a ofishin sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel