Da duminsa: Dalibai 44,497 sun samu nasarar cin jarabawar NECO ta shekarar 2018

Da duminsa: Dalibai 44,497 sun samu nasarar cin jarabawar NECO ta shekarar 2018

- NECO, ta saki sakamakon jarabawar SSCE da dalibai suka zana a zangon Nuwamba/Disamba, 2018

- A cewar sanarwar, dalibai 59,963 ne suka yi rejistar zana jarabawar akan darussa 28

- Ya ce dalibai 37,069 da ke wakiltar kashi 62.48 suka samu nasara a darussa biyar da suka hada da lissafi da turanci

Hukumar da ke kula da zana jarabawar kammala makarantar sakandire ta kasa, NECO, ta saki sakamakon jarabawar SSCE da dalibai suka zana a zangon Nuwamba/Disamba, 2018.

Bayanin hakan na kunshe a cikin wata sanarwa da hukumar ta rabawa manema labarai a ranar Juma'a ta hannun magatakardar hukumar NECO, Abubakar Gana.

A cewar sanarwar, dalibai 59,963 ne suka yi rejistar zana jarabawar akan darussa 28.

KARANTA WANNAN: Zargin sace N4.6bn: Kotu ta wanke tsohon gwamnan Oyo da kwamishinansa

Da duminsa: Dalibai 44,497 sun samu nasarar cin jarabawar NECO ta shekarar 2018

Da duminsa: Dalibai 44,497 sun samu nasarar cin jarabawar NECO ta shekarar 2018
Source: Depositphotos

Mr Gana ya ce daga cikin dalibai 57,842 da suka zauna suka zana jarabawar darasin Turanci, 44,497 da ke wakiltar kashi 76.93 ne kadai suka samu masarar samun makin 'Credit'.

"Dalibai 57,275 ne suka zana jarabawar darasin Lissafi, inda dalibai 47,151 ne kawai suka samu nasara da makin 'Credit' ko 'Distinction''.

Ya ce dalibai 37,069 da ke wakiltar kashi 62.48 suka samu nasara a darussa biyar da suka hada da lissafi da turanci.

Haka zalika, dalibai 47,031 da ke wakiltar kashi 79,27 suka samu nasarar haye darussa biyar, walau da Lissafi ko Turanci ko babu darussan biyu.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel