Kamfen din Atiku a Benue: Filin wasa na Aper Aku ya cika ya batse, hotuna

Kamfen din Atiku a Benue: Filin wasa na Aper Aku ya cika ya batse, hotuna

A yau Juma'a 8 ga watan Janairu ne dan takarar shugabancin kasa karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya isa jihar Benue domin kaddamar da yakin neman zabensa.

Al'umma da dama sun fito domin nuna kauna da goyon baya da Atiku da tawagarsa yayin da suka isa filin wasa na Aper Aku da ke Makurdi.

Atiku ya yiwa mutan Benue alkawarin zai tabbatar da tsaron rayyuka da dukiyoyinsu tare da inganta noma idan suka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

A cewar kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, Atiku ya yi wannan alkawarin ne yayin da ya ke jawabi a wurin kaddamar da yakin neman zaben a Makurdi.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma yi alkawarin kare dukkan dokokin da bangarorin gwamnati uku suka kafa.

Ga hotunan yadda yakin neman zaben ya kasance a kasa:

Yadda yakin kamfen din Atiku ta kasance a jihar Benue, hotuna

Dan takarar shugabancin kasa na PDP, Atiku Abubakar a kan mimbari kafin ya fara jawabi ga magoya bayansa a garin Makurdi
Source: Twitter

Yadda yakin kamfen din Atiku ta kasance a jihar Benue, hotuna

Atiku Abubakar yayin da ya ke jawabi ga dubban magoya bayansa a wurin taron kamfen dinsa a Makurdi na jihar Benue
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Kamfen: Taron Atiku a jihar Borno ya bayar da mamaki, hotuna

Yadda yakin kamfen din Atiku ta kasance a jihar Benue, hotuna

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, Shugaban PDP na kasa, Uche Secondus, Atiku Abubakar da sauran jiga-jigan jam'iyyar PDP a wurin kamfen a jihar Benue
Source: Twitter

Yadda yakin kamfen din Atiku ta kasance a jihar Benue, hotuna

Dan takarar shugabancin kasa na PDP, Atiku Abubakar yayin da ya ke shigowa filin taron kamfen a garin Makurdi na jihar Benue
Source: Twitter

Yadda yakin kamfen din Atiku ta kasance a jihar Benue, hotuna

Dubban magoya bayan Atiku Abubakar da jam'iyyar PDP na jihar Benue da suka hallarci kaddamar da yakin neman zabe a yau Juma'a.
Source: Twitter

Yadda yakin kamfen din Atiku ta kasance a jihar Benue, hotuna

Yadda yakin kamfen din Atiku ta kasance a jihar Benue, hotuna
Source: Twitter

Yadda yakin kamfen din Atiku ta kasance a jihar Benue, hotuna

Yadda yakin kamfen din Atiku ta kasance a jihar Benue, hotuna
Source: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel