Jerry Gana ya yi watsi da goyon bayan Buhari da SDP tayi

Jerry Gana ya yi watsi da goyon bayan Buhari da SDP tayi

- Jigo a jam'iyyar SDP da ke neman takarar shugabancin kasa a jam'iyyar, Jerry Gana ya nuna kin amincewarsa da goyon bayan Shugaba Buhari da jam'iyyar tayi

- Gana da magoya bayansa sun ce wasu tsiraru ne da ke biyaya ga Donald Duke da Alhaji Shehu Gabam suka dauki matakin ba tare da neman amincewar anihin 'yan majalisar zartarwa na jam'iyyar ba

- Jerry Gana da magoya bayansa na G 19 sun ce za su gana a ranar Litinin domin daukan mataki a kan abinda suka kira cin amana

Tsohon Ministan Sadarwa, Farfesa Jerry Gana ya nuna kin amincewarsa game da goyon bayan da jam'iyyarsa ta Social Democratic Party (SDP) ta bawa Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin dan takarar ta za ta zaba a zaben da ke tafe.

Gana da 'yan kungiyar yakin neman zabensa na G 19 sunyi Allah wadai da matakin da jam'iyyar ta SDP ta dauka abinda ta kira cin amana kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Jerry Gana ya yi watsi da goyon bayan Buhari da SDP tayi

Jerry Gana ya yi watsi da goyon bayan Buhari da SDP tayi
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Jigo a APC ya ce kowa ya zabi abinda ya ke so bayan zaben Buhari

A yayin da ya ke yiwa manema labarai jawabi a ranar Juma'a a Abuja, Shugaban G 19, Dr Ike Neliaku ya ce ba a gayyaci mafi yawancin mambobin kwamitin zartarwa na jam'iyyar zuwa wurin taron da akayi ba.

Neliaku ya ce: "A kan abubuwan da ke faruwa a jam'iyyar mu cikin kwanakin nan, muna son mu sanar da 'yan Najeriya cewa muyi mamakin jin cewa wasu tsirarun marasa kishin jam'iyyar mu sunyi taro a Abuja sun zabi dan takarar shugabancin kasa na APC a matsayin wanda za su marawa baya.

"Muna so mu tabbatar wa al'umma cewa bamu tare da su kuma abinda suka aikata ya jefa sauran 'yan takarar jam'iyyar mu cikin tsaka mai wuya. Wadanda suka aikata wannan cin amanar magoya bayan Donald Duke da Alhaji Shehu Gabam ne.

"Muna so mu sanar cewa ainihin 'yan majalisar zartarwa na jam'iyyar mu basu hallarci taron ba wasu kuma ba a ma gayyace su ba. Anyi amfani da wasu mutane na bogi ne a maimakonsu domin cimma wata buri na kwadayin abin duniya."

G 19 din ta ce za ta yi taro a ranar Litinin domin daukan mataki a kan wannan abinda ta kira cin amana da ba za ta amince da shi ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel