Sojoji sun kashe 'yan Boko Haram masu yawa a Mallam Fatori, hotuna

Sojoji sun kashe 'yan Boko Haram masu yawa a Mallam Fatori, hotuna

- Dakarun sojojin Najeriya sun kashe mayakan Boko Haram masu yawa a wani musayar wuta da su kayi a Mallam Fatori

- Sojojin sun kuma yi nasarar kwato bindigu, alburusai, gurneti da wasu muggan makamai daga hannun 'yan ta'addan

- Rundunar sojin ta yi kira ga al'umma da su rika kaiwa sojojin rahoton duk wani abinda ba su gamsu da shi ba domin a dauki mataki cikin gaggawa

A cigaba da kakabo ragowar 'yan ta'addan da su kayi saura a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya, Dakarun Sojin Najeriya karkashin rundunar Operation Lafiya Dole da ke Mallam Fatori a jihar Borno sunyi nasarar halaka wasu 'yan ta'ada masu yawa yayin wani musayar wuta da su kayi.

Sojoji sun kashe 'yan ta'adda masu yawa a Mallam Fatori, hotuna

Sojoji sun kashe 'yan ta'adda masu yawa a Mallam Fatori, hotuna
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Ruwan wuta: Sojojin sama sun kashe 'yan bindiga da dama a Zamfara

Sojojin sun koro 'yan ta'addan daga mabuyarsu da ke Tumbun Gini inda suka fito motocci da babura 10. Sojojin sunyi galaba a kan 'yan ta'addan inda suka kashe da dama cikinsu. Sojin Saman Najeriya sun kashe wadanda su kayi yunkurin tserewa.

Sojoji sun kashe 'yan ta'adda masu yawa a Mallam Fatori, hotuna

Sojoji sun kashe 'yan ta'adda masu yawa a Mallam Fatori, hotuna
Source: Facebook

Sojojin kuma sunyi nasarar kwato bindigu, alburusai, gurnetin hannu da wasu muggan makamai daga hannun 'yan ta'addan.

Sojoji sun kashe 'yan ta'adda masu yawa a Mallam Fatori, hotuna

Sojoji sun kashe 'yan ta'adda masu yawa a Mallam Fatori, hotuna
Source: Facebook

Sanarwar ta fito ne daga bakin mataimakin direktan watsa labarai na rundunar soji na sector 3, Kwanel Ezindu Idimah.

Wannan shine karo na biyu cikin kwanaki 5 da rundunar Sector 3 na Operation Lafiya Dole ke saman galaba a kan mayakan Boko Haram. Na farkon ya faru ne a ranar 2 ga watan Fabrairu a Tumbin Gini.

Wannan na zuwa ne bayan ziyarar da kwamandan sector 3 ya kai a sansanin na Mallam Fatori domin karfafawa sojojin gwiwa a ranar 4 ga watan Fabrairu. Ya shawarci sojojin su cigaba da nuna jarumta wurin aikinsu tare da biyaya ga kasarsu.

Ya kuma yi kira ga al'umma da su rika kaiwa sojojin rahoton duk wani abinda ba su gamsu da shi ba domin a dauki mataki cikin gaggawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel