Wata mata tayi wa mijinta wanka da tafasashen ruwan barkono

Wata mata tayi wa mijinta wanka da tafasashen ruwan barkono

Wata mata mai shekaru 32 da aka ambata da suna, Misis Rebecca Efeitima, daga yankin Amukpe, da ke Sapele a jihar Delta a ranar Talata ta watsa ma mijinta mai sekaru 43 tafasashen ruwan barkono.

Mijin nata mai suna Monday Efeitima ya bayyana cewa bai samu kowani sabani da matar tashi ba sannan cewa da farko so tayi ta bashi guba amma bata cimma nasara ba, don haka ta yanke sawarar nakasa shi.

Wanda abun ya cika dashi yace: “Matsalar ya fara ne a ranar Talata. Ba zan iya tuna ko mun samu sabani da ita ba amma dai kawai ina zaune bayan na dawo daga aiki sai ta kawo mani abinci dn naci. Hakan ya bani mamaki domin bata saba yimun haka ba.

Wata mata tayi wa mijinta wanka da tafasashen ruwan barkono

Wata mata tayi wa mijinta wanka da tafasashen ruwan barkono
Source: Depositphotos

“Yawancin lokuta, idan na dawo daga aiki sai na roke ta abinci kafin ta kawo. Don haka sai na shiga kokwanto, naki cin abincin.

“Don kawai a zauna lafiya, sai na zubar da abincin bayan ta siga wanka sannan da ta dawo, sai ta zauna tare dani sannan ta fara tambayan ko ina jin wani abu, na fada mata a’a.

“Sai ta fita waje, ta samu ruwa mai zafi, ta zuba barkono sannan ta watsa mun ruwan ina cikin bacci.”

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa wannan ba shine karo na farko da Rebecca ta yi yunkurin kashe mijin nata ba.

K KARANTA KUMA: Zaben 2019: Atiku, PDP na shirin shigo da makamai da kudade ta Kamaru - Nabena

Wani makwabcinsu yace: “Wannan abu ne da ta saba, ta sha yin yunkurin kashe shi ba tare da ta cimma nasara ba, don haka ba abun mamaki bane a wajen mu.

“Matsalarsa ya cika son matar da yawa. Ta so bashi guba a watan Nuwamban shekarar da ya gabata amma sai ta karkare dab a danta na farko da ta Haifa da wani guban.

“Da muka bashi shawarar ya rabuda matar sai yace zai ci gaba da zama da ita saboda suna da yara uku tare. Yanzu kuma ga abun da tayi mashi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel