Sakamakon zaben Najeriya na da matukar muhimmaci a gare mu - Amurka

Sakamakon zaben Najeriya na da matukar muhimmaci a gare mu - Amurka

Kasar Amurka ta bayyana cewa sakamakon zaben gama gari da za'a gudanar nan ba da dadewa a tarayyar Najeriya yana da matukar muhimmaci a gareta da ma dukkan daukacin kashen duniya baki daya.

Jakadan kasar ta Amurka a kasar Najeriya Mista Stuart Symington shi ne ya bayyana hakan jim kadan bayan ya kammala wata ganawar sirri da gwamnan jihar Nasarawa, Gwamna Tanko Al-makura a ofishin sa.

Sakamakon zaben Najeriya na da matukar muhimmaci a gare mu - Amurka

Sakamakon zaben Najeriya na da matukar muhimmaci a gare mu - Amurka
Source: UGC

KU KARANTA: Tsohon dogarin Tinubu ya zama kwamishinan 'yan sandan Kwara

Legit.ng Hausa ta samu cewa Mista Stuart Symington ya kara da cewa ya zama dole kasar ta Najeriya ta shirya zabukan zabukan ta cikin gaskiya da amana kuma sakamakon yayi daidai da ra'ayin 'yan kasar domin kaucewa dukkan fitina.

A wani labarin kuma, kasar ta Amurka ta yi babban gargadi ga bangarorin siyasa a Najeriya kan makomar zaben kasar na 2019.

Wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar a shafinta na twitter, ta ce dole ne jami'an tsaron Najeriya su tabbatar da zaman lafiya domin al'ummar kasar su samu damar 'yancisu.

Ta kuma yi kira ga bangarorin siyasa a Najeriya, musamman hukumar zabe da su tabbata zabukan da za a yi a mako mai zuwa ya kasance an tsaftace shi daga dukkan wata matsin lamba daga gwamnati ko barazana daga kasashen waje.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel