Hukuncin nan take: Fusatattun matasa sun kashe wani matashi bayan ya kashe mahaifiyarsa

Hukuncin nan take: Fusatattun matasa sun kashe wani matashi bayan ya kashe mahaifiyarsa

Rundunar Yansandan jahar Enugu ta sanar da mutuwar wani mutumi a hannun gungun fusatattun matasa bayan shima mutumin ya yi ma mahaifiyarsa da ta yi nakudarsa har ta tsugunna ta haifeshi, kisan gilla a jahar Enugu.

Majiyar Legit.ng ta labarto cewa wannan lamari mai muni ya faru ne a unguwar Isiagu Ibagwa dake cikin karamar hukumar Igboeze ta kudu na jahar Enugu, kamar yadda kaakakin rundunar Yansandan jahar, SP Ebere Amaraizu ya bayyana.

KU KARANTA: Zaben 2019: Gwamnatin tarayya za ta kulle makarantu 109 don gudun ko-ta-kwana

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Juma’a 8 ga watan Feburairu, SP Ebere ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin data gabata, da misalin karfe 1:30 na rana, inda wani matashi mai suna Ifesinachi ya daddatsa babarsa.

“Hankula sun tashi a garin Isiagwu Ibagwa yayin da wani matashi mai suna Ifesinachi Ukweze ya halaka babarsa mai suna Beatrice Ukwueze ta hanyar yim amfani adda wajen sassareta akan wata tirka tirka da haryanzu bamu tabbatar da ita ba.

“Wannan mataki da Ifesinachi Ukwueze ya dauka akan mahaifiyarsa ne ya harzuka sauran matasan unguwar, inda nan da nan suka afka masa, yadda ko kafin isowar Yansanda har sun kashe shi.” Inji Kaakaki Ebere.

Daga karshe Kaakaki Ebere yace tuni sun mika gawar uwar da danta zuwa dakin ajiyan gawarwaki na babban asibitin karamar hukumar, sa’annan ya kara da cewa sun kaddamar da bincike akan lamarin don gano musabbabin abinda ya janyo fitinar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel