Yanzu yanzu: Babu wani hanya da za a rufe saboda ziyarar Buhari – Gwamnatin Lagas

Yanzu yanzu: Babu wani hanya da za a rufe saboda ziyarar Buhari – Gwamnatin Lagas

- Gwamnatin jihar Lagas ta sanar da cewa babu hanyar da za a rufe a jihar saboda ziyarar Shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Mista Lawanson yace ayyuka za su gudana a hanyoyin jihar kamar yadda aka saba

- Sai dai ya bukaci mazauna da su janyee daga filin wasa na Teslim Balogun inda Shugaban kasar zai gudanar da gangamin kamfen dinsa idan har basu da abun yi a yankin

Gwamnatin jihar Lagas ta sanar da cewa babu hanyar da za a rufe a jihar saboda ziyarar Shugaban kasa Muhammadu Buhari na ranar Asabar, 9 ga watan Fabrairu.

Kwamishinan sufuri na jihar, Mista Ladi Lawanson ya bayar da sanarwa a yau Juma’a, 8 ga wata Fabrairu.

Yanzu yanzu: Babu wani hanya da za a rufe saboda ziyarar Buhari – Gwamnatin Lagas

Yanzu yanzu: Babu wani hanya da za a rufe saboda ziyarar Buhari – Gwamnatin Lagas
Source: UGC

Daga cikin hanyoyin da aka sanar cewa za a rufe sun hada da: Funsho Williams Avenue, Surulere Lawanson/Itire /Tejuosho road Apapa/Costain road Abebe village Eric Moore road Eko Bridge/Apongbon Marina road Ikorodu road Mobolaji Bank Anthony way Old Toll Gate/Third Mainland Bridge/Obalende Airport road Oshodi-Oworonshoki expressway Agege Motor road Jibowu area Yaba/Muritala Mohammed way Iddo/Otto Herbert Macaulay way Adekunle and Ijora Olopa.

KU KARANTA KUMA: Zaben Shugaban kasa: Dalilin da yasa SDP ta yi watsi da dan takararta ta dauki Buhari

Amma kwamishinan sufuri, Mista Lawanson yace ayyuka za su gudana a hanyoyin jihar kamar yadda aka saba.

Sanan ya bukaci mazauna da su janyee daga filin wasa na Teslim Balogun inda Shugaban kasar zai gudanar da gangamin kamfen dinsa idan har basu da abun yi a yankin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel