Da dumi dumi: Yan bindiga sun yi garkuwa da wani dan majalisa a jahar Sakkwato

Da dumi dumi: Yan bindiga sun yi garkuwa da wani dan majalisa a jahar Sakkwato

Abin da takaici, ace har yanzu wasu yan tsirarun miyagun mutane masu garkuwa da mutane sun gagari hukuma a jahar Zamfara da jahar Sakkwato, suna cin karensu babu babbaka ba a akan talakawan ba, ba akan attajiran ba.

A nan ma wasu gungun yan bindiga ne suka yi awon gaba da wani dan majalisar dokokin jahar Sakkwato, Honorabul Sani Yakubu na jam’iyyar APC dake wakiltar karamar hukumar Gudu a majalisar dokokin jahar.

KU KARANTA: Zaben 2019: Gwamnatin tarayya za ta kulle makarantu 109 don gudun ko-ta-kwana

Da dumi dumi: Yan bindiga sun yi garkuwa da wani dan majalisa a jahar Sakkwato

Sani Yakubu
Source: UGC

Yan bindigan sun yi awon gaba da Sani Yakubu ne da nufin yin garkuwa dashi, tare da cigaba da rikeshi har sai iyalansa sun biyasu kudin fansa da suka tayar ma miliyoyin nairori, kamar yadda suka saba, musamman duba da cewa dan majalisa ne.

Sai dai majiyar Legit.ng ta ruwaito ba Sani Yakubu kadai masu garkuwan suka sace ba, harda wani abokinsa, amininsa, kuma abokin tafiyarsa, inda suka taresu a daidai lokacin da suke kan hanyar zuwa garin Balle daga garin Tangaza.

A wani labari kuma, yan bindiga sun kashe wasu mutane goma sha hudu da basu ji ba, basu gani ba a garin Tudun Wadan Mai Jatau a jahar Zamfara, daga cikin wadanda suka kashe har da yayar Sanata Kabiru Marafa.

Bayan ga bindige yayar Sanatan, wanda aka fi sani da suna Hajiya Sa’adatu Ahadi, sa’annan yan bindigan sun yi awon gaba da Maigidanta da nufin yin garkuwa da shi, har sai an biyasu kudin fansa.

Wannan kisa da aka yi ma Hajiya Sa’adatu Ahadi ya yi matukar dimauta Sanata Marafa, wanda yace itace babbar yayarsu, kuma itace ta rikeshi tun yana karami, don haka tamkar mahaifiya take a wajensa sakamakon kyakkyawar kulawar da ta bashi yayin da yake tasowa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel