Boko Haram: Yankin mazaba ta yanzu babu matsalar tsaro - Sanata Binta ta Adamawa

Boko Haram: Yankin mazaba ta yanzu babu matsalar tsaro - Sanata Binta ta Adamawa

- Al'ummar jihar Adamawa zasu gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali bayan Boko haram sunkai musu hari

- An karayata jita-jita na cewa jam'iyar adawa tana amfani da boko haram akan sha'anin zabe

- Ba yadda za'ayi jam'iyar mu ta rusa kanta bayan shafe shekaru tana gina kanta

Boko Haram: Yankin mazaba ta yanzu babu matsalar tsaro - Sanata Binta ta Adamawa

Boko Haram: Yankin mazaba ta yanzu babu matsalar tsaro - Sanata Binta ta Adamawa
Source: Facebook

Sakamakon hare-haren Boko Haram a kauyukan shuwa da Kirchinga na jihar Adamawa, sanata mai wakiltar Adamawa ta arewa, Sanata Binta Garba, tace ana zuzuta harin ne fiye da faruwar shi a kafafen yada labarai.

Da ta zanta da manema labarai a gidanta dake Yola, sanatan tace garuruwan Michika da Madagali suna lafiya lau kuma shirye don zabe mai gabatowa.

A don haka ne tace, ba gaskiya bane da ake yadawa na cewa jam'iyya mai mulki na assasa aiyukan Boko Haram don hargitsa zabe mai zuwa.

GA WANNAN: Ma'aikatan jihar Adamawa sun zargi Bindow da kamfe da kudaden albashinsu

"Babu wanda zai ce aiyukan gyara da jam'iyyata tayi zata kuma zo rana tsaka ta lalata da hannun ta. Idan ba don jam'iyyata ba, mutane da yawa da basu gidajen su yanzu. Jita jitan bata da makama balle tushe. Ina tabbatarwa da jama'a cewa za'ayi zabe a ko'ina na yankin," inji Mrs Garba.

Adamawa da sauran yankunan arewa maso gabas sun taba zama karkashin Boko Haram, wadanda suka sanya tsattsauran ra'ayin Islama a matsayin shari'ar da zasu yi aiki da ita.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel