Yanzu-yanzu: Kotun koli ta yanke hukunci na karshe, babu APC a zaben jihar Rivers na bana

Yanzu-yanzu: Kotun koli ta yanke hukunci na karshe, babu APC a zaben jihar Rivers na bana

Kotun kolin Najeriya ta tabbatar da hukuncin babban kotun jihar RIbas dake zanne a Port Harcourt wacce tayi watsi da dukkan zabukan fidda gwanin da jami'yyar All Progressives Congress (APC) ta gudanar a jihar Ribas.

Alkalan kotun karkashin Jastis Mohammed Dattijo a ranan Juma'a sun yi watsi da takardan bangaren ministan sufuri, Rotimi Amaechi, wacce ts shigar da kara kotun daukaka kara.

Mun kawo muku a baya cewa kotun daukaka kara dake birnin Fatakwal ta bada umurnin dakatad da aiwatar da hukuncin babban kotun tarayya da ta bayar na watsi da zabubbukan fidda gwani da jam'iyyar All Progressives Congress, shiyar jihar Ribas ta gudanar.

Tun lokacin, kotun ta haramtawa hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC sanya jam'iyyar APC da yan takaranta a takardan kuri'a na jihar RIbas a zaben 2019.

A ranan 7 ga watan Junairu, Jastis Kolawole Omotosho ya yi watsi da dukkan zaben fidda gwani tsakanin bangaren Magnus Abe da Tonye Cole.

Yanzu haka, kakakin yakin neman zaben gwamnan jihar RIvers, Mista Tonye Princewill, ya bayyana cewa ba zai yiwu a gudanar da zabe a jihar Rivers ba tare da jam'iyyar APC ba, saboda haka, hukumar INEC ta daga zaben.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel