Kyan yaba alheri, riqe amana: Masu fanshon Nigeria Airways sun shirya wa zaben makon gobe tsaf!

Kyan yaba alheri, riqe amana: Masu fanshon Nigeria Airways sun shirya wa zaben makon gobe tsaf!

- Tsaffin ma'aikatan Nigeria Airways ('yan fansho) sun fito suna gangamin nuna goyan bayansu ga takarar Buhari

- A ranar Juma'a filin tashi da saukar jiraje na Murtala Muhammad ya tumbaza da magoya baya

- Sun fito wannan gangami ne don nunawa Buhari godiyar su bisa tsamosu daga halin da suke ciki

Kyan yaba alheri, riqe amana: Masu fanshon Nigeria Airways sun shirya wa zaben makon gobe tsaf!

Kyan yaba alheri, riqe amana: Masu fanshon Nigeria Airways sun shirya wa zaben makon gobe tsaf!
Source: Depositphotos

Tsaffin ma'aikatan da 'yan fanso sun bayyana cewa suna goyan bayan Buhari ne bisa biyansu kudin su N22.6b da yayi a watan Octobar shekara ta 2018. Dama dai APC din tayi alkawarin biyan masu bin gwamnati bashinsu da haakkokinsu.

Da yake magana da yawun tsaffin ma'aikatan Mr Lookman Animashaun yace sun fito wannan gangami ne dan su nuna godiyar su ga shugaban kasar bisa abinda yayi musu.

Yace "Bamu da bakin nuna godiya ga shugaban kasa Muhammad Buhari ya biya fan fanso da tsaffin ma'aikatan jirgi 6,000 kudin su".

"Shekaru 14 kenan muna cikin wannan hali sai zuwansa muka samu yanci."

GA WANNAN: An kaddamar da jirgin kasan nan da kasar Yarabawa suka dade suna jira, nan gaba zai je har Daura

"Wasu daga cikin mu wanda zasukai 8,000 sun rasa rayukansu a lokacin da suke cikin halin kakanikayi akan a biyasu hakkin su".

"Amma yanzu Muhammad Buhari ya share mana hawayen mu ta hanyar biyanmu hakkin mu.

Wannan dalili ya sanyamu fitowa dan mu nuna godiyar mu sannan mu bayyana goyan bayan mu bisa kara tsayawar sa takarar shugabancin kasar nan."

Shugaba Buhari dai na neman zagayen karshe a zaben 2019 dinnan.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel