Wannan lamari yana daga min hankali matuqa-gaya - Abdulaziz Yari na Zamfara

Wannan lamari yana daga min hankali matuqa-gaya - Abdulaziz Yari na Zamfara

- Gwamna Yari ya nuna damuwar shi kan yadda ake garkuwa da mutane ta zamo sana'a a jihar Zamfara

- Yayi kira ga sarakunan gargajiya da masu gidajen haya dasu sa ido akan baki da kanzo su rude su da kudi don samun matsuguni

- Ya roki 'yan jihar dasu fito kwansu da kwarkwata don zaben dan takara ra'ayin su

Wannan lamari yana daga min hankali matuqa-gaya - Abdulaziz Yari na Zamfara

Wannan lamari yana daga min hankali matuqa-gaya - Abdulaziz Yari na Zamfara
Source: Facebook

Gwamna Abdulaziz Yari na jihar Zamfara yace ya shiga damuwa sakamakon cigaban garkuwa da mutane "da ya zama kasuwanci mafi ci a jihar".

Yari ya sanar da hakan ne ga mutanen karamar hukumar Maradun ta jihar lokacin da ya kai ziyara ga sarkin Maradun, Alhaji Garba Tambari a fadar shi.

Gwamnan ya ziyarci basaraken ne a cigaba da yakin neman quri'u da ma jajantawa jama'arsa kan matsalar tsaro.

Wannan lamari yana daga min hankali matuqa-gaya - Abdulaziz Yari na Zamfara

Wannan lamari yana daga min hankali matuqa-gaya - Abdulaziz Yari na Zamfara
Source: UGC

Ofishin dillancin labarai na NAN, ya ruwaito cewa jihar Zamfara dake yankin arewa maso yamman kasar nan na fama da kashe kashe da kuma harin fulani makiyaya wanda ya lamushe daruruwan rayuka a cikin shekarun nan.

"Banga yiwuwar garkuwa da mutane zaizo karshe a jihar Zamfara ba saboda masu yin ma sun maida shi kasuwanci mai zaman kanshi. Masu gidaje na bada hayar su ga duk wanda wanda ya nema, ballantana wadanda suka cika su da kudi,"

"A don haka ne yan ta'adda suke samu zartar da shirin su a gidajen da suka karba haya,"

"Naso ace kiran da nayi na farko ga sarakunan gargajiya na su saka ido akan bakin dake zuwa su zauna da kuma masu gidajen haya su binciki masu neman haya kafin badawa kuma kada kudi ya jasu yayi amfani," inji shi.

GA WANNAN: Biyo bayan alkalumma dake nuna wai Atiku ne zai lashe jihohin tsakiyar Najeriya sun fara yawo, martani daga Nassarawa

Gwamnan ya jinjinawa aiyukan jami'an tsaro da kuma 'yan taimakon kai da kai da suka fara a watan Nuwamba da ta were a jihar don fada da laifuka a jihar.

Yari ya roki mazauna jihar ta Zamfara dasu fito kwan su da kwarkwatar su a ranar zabe don saka kuri'a ga dan takarar da suke ra'ayi.

A maida martanin Tambari, ya tabbatarwa da gwamnan cewa yan jihar zasu fito a ranar zabe don hakan aikin su ne a matsayin yan kasa.

A makon jiya ne dai aka gano gwamna a taro yana mallakawa wata kungiyar addini kudi tsababa a buhu, lamari da ya sanya wasu ke ganin harkar tsaro ce ya kamata ta lakume kudin.

An sha jin Gamnan yana kuma cewa yawan zunubbai ne ya janyo matsalolin dake addabar jihar, nan ma kuma an masa caa, musamman daga kudancin Najeriya.

Kashe-kashen dai babu alamar zasu sassauta, duk da karin sojoji a jihar a kwanakin baya.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel