Onnoghen da CJN Muhammed sun amsa takardar tuhumarsu da majalisin Alkalai na kasa ya basu mako daya su amsa

Onnoghen da CJN Muhammed sun amsa takardar tuhumarsu da majalisin Alkalai na kasa ya basu mako daya su amsa

- Dakataccen alkalin alkalai da mukaddashin alkalin alkalai sun maida martani

- Ana zargin dakataccen alkalin alkalan da laifin kin bayyana kadarar shi wanda yace hakan aikin mantuwa ne

- Mukaddashin alkalin alkalai Mohamed ana zargin shi da mika kanshi a rantsar dashi ba tare da yarjewar NJC ba

Shekaru 15 ga saurayi da jaraba ya kai lalata da akuya

Shekaru 15 ga saurayi da jaraba ya kai lalata da akuya
Source: UGC

Dakataccen alkalin alkalan Najeriya, Walter Onnoghen da mukaddashin alkalin alkalai sun amsa tuhumar da hukumar shari'a ta kasa ta tura musu, wadda ake kira Majalisin koli na alkalai a kotunan Najeriya, watau Judicial Council.

A takardun korafin na makon jiya, an tuhume su da kowanne ya bada bahasi kan zargin da ake masa na yin ba daidai ba.

Shi Alkalin Alkalai, ya bada bahasin me yasa ya yarda shugaba Buhari ya rantsar dashi, shi kuma tsohon CJN din yayi bayani kan kudaden da wai ya manta biliyoyi a asusunsa.

Onnoghen da CJN Muhammed sun amsa takardar tuhumarsu da majalisin Alkalai na kasa ya basu mako daya su amsa

Onnoghen da CJN Muhammed sun amsa takardar tuhumarsu da majalisin Alkalai na kasa ya basu mako daya su amsa
Source: UGC

Majalisin Alkalan, yayi taron ta a ranar talata 29 ga watan Janairu inda ya umarci Onnoghen da ya maida martani akan takardar qorafi, watau Petition da Zikhrillahi Ibrahim na Resources Centre for Human Rights and Civil Education, inda shi kuma mai shari'a Alkalin Alkalai Mohammed aka umarce shi da ya maida martani ga takardu biyu na Center for Justice and Peace Initiative da Olisa Agbakoba ya rattabo.

Takardar ta dakataccen mai shari'a Onnoghen akan zargin shi da rashin bayyana kadarar shi wanda shine a gaban kotun manyan laifuka a Abuja bayan takarda ta farko da Dennis Aghanya na Anti-Corruption and Research Based Data Initiative (ARDI).

Shi kuma mukaddashin alkalin alkalan Mohammed na fuskantar zargi daga Agbakoba akan mika kanshi da yayi aka rantsar dashi ba tare da sanin NJC ba.

Martanin da suka maida a ranar juma'a 5 ga watan Fabrairu wanda ba a bayyanawa mutane ba, amma mai shari'a Onnoghen ya bayyanawa CCT cewa mantuwa ce tasa bai bayyana kadarorin nashi ba.

GA WANNAN: Masu gudun hijira ma zasu dangwala quri'unsu kamar kowa, a sansanoninsu - INEC

A halin yanzu NJC zatayi taro don duba martanin masu shari'ar biyu a ranar litinin 11 ga watan Fabrairu.

Wani ma'aikacin da yasan halin da NJC take ciki yace kafin taron, za a iya hada kwamitin mutane biyar don kara duba martanin kafin mika shi ga kungiyar.

"Idan NJC bata gansu da martanin ba,zasu iya kafa wani kwamitin. Hakan zai dau fiye da kwanaki biyu," inji majiyar mu.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel