An kaddamar da jirgin kasan nan da kasar Yarabawa suka dade suna jira, nan gaba zai je har Daura

An kaddamar da jirgin kasan nan da kasar Yarabawa suka dade suna jira, nan gaba zai je har Daura

- Gwamnatin tarayya ta dauki alkawarin samar da hanyar jirgin kasa daga Legas zuwa Ibadan

- Mataimakin shugaban Yemi Osinbajo ne yayi wannan batu a yau da safe a tashar Iju dake jihar Legas

- Hanyoyi zasuyi karko matukar za'a dunga daukar kaya ta hanyar jirgin kasancewa Oba Gbadebo

An kaddamar da jirgin kasan nan da kasar Yarabawa suka dade suna jira, nan gaba zai je har Daura

An kaddamar da jirgin kasan nan da kasar Yarabawa suka dade suna jira, nan gaba zai je har Daura
Source: Depositphotos

A yau ne gwamnatin tarraya ta dauki alkawarin karasa samar da hanyar jirgin kasa daga Legas zuwa arewa wanda ake kaddamar da sashen farkonsa a yau.

Mataimakin shugaban kasa Professor Yemi Osinbajo ne yayi wannan alkawari a tashar jirgin da yake budewa dake Iju a yau da safe.

Oba Gbadebo wanda ya halarci wajen kaddamarwar a Iju dake jihar Legas ya bayyanawa manema labarai cewa tun a shekara ta 1900 da aka dauki wannan alkawari na samar da hanyar jirgin kasa daga Legas zuwa Kano amma ba'a kara bi takanta ba.

Amma yanzu an sake daukar alkawarin gudanar da wannan aiki na samar da hanya mai tsayin kilomita 156 daga Legas zuwa Ibadan,sarki yace tarihi ne yake maimata kansa.

GA WANNAN: Amana ta wadanda na taimaka suka ci - Rochas

A bangaren sarkin yace wannan cigaba da aka samu zai kawo taimakawa tattalin arzikin arewa maso gabashin kasar.

Ya kara da cewa alkawarin gudanar da wannan aiki anyi shine shekaru 116 da suka gabata ba'a samu cikashi ba.

Ya kara da cewa hanyoyi zasuyi karko idan ana daukar kaya ta hanyar jirgin kasa.

Wannan karon dai Yarabawa sun caba, kuma dama ana so ayi hakan kafin zaben 2019 a makon gobe.

Shafin NAIJ.com Hausa ne ya koma LEGIT.ng Hausa

Latsa kuga sabuwar manhajar Legit.ng Hausa a wayarku ta salula: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafukanmu na dandalin sada zumunta sune:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel